Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR Birnin Kebbi
An bayyana sakamakon sabon zaɓen fidda gwani na ɗan takaran APC na majalisar wakilai ta tarayya, mazaɓar Argungu/Augie, jihar Kebbi.
Umar Hassan ya samu ƙuri’a 33013 a zaɓen da aka gudanar ranar, inda ya doke abokin takararsa, Samir Salihu Felande, wanda ya samu ƙuri’a 1319.
Shugaban kwamitin gudanar da zaɓen, wanda kuma shine jami’in ayyana sakamako, tsohon kakakin majalisar dokokin Jihar Bauchi, Rt. Hon. Shehu Kawu Damina, ya ce, Umar Hassan Augie shi ya samu mafi rinjayen ƙuri’a, kuma ya cika dukan ƙa’idojin zaɓe.
Rt. Hon. Damina ya ce, a matsayinsa na jami’in ayyana sakamakon zaɓe, Umar Hassan Augie shi ne ya yi nasara, kuma tabbataccen wanda aka zaɓa a matsayin ɗan takarar APC na mazabar majalisar Argungu da Augie a zaɓen 2027.
Da ya ke jawabin godiya, zaɓaɓɓen ɗan takaran, Umar Hassan Augie, ya jinjina ma duk masu ruwa-da-tsaki wurin gudanar da zaɓen, aka kammala shi cikin kwanciyar hankali da nasara.
Augie ya gode ma dukan ‘yan jam’iyyar APC, sannan kuma ya miƙa ma abokin takararsa goron gayyata ya zo ayi tafiya tare da shi, da nufin samun nasarar APC a zaɓen 2027.
Babban kotun tarayya da ke zamanta a Birnin Kebbi ta soke zaɓen da aka gudanar tun kusan wata uku da suka wuce, sanadiyyar ƙarar da Samir ya shigar, yana ƙalubalantar sakamakon zaɓen, sannan ta bada umurnin a sake wani sabon zaɓen fidda ɗan takara.
