Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Dan takarar Shugaban ƙasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC), Omoyele Sowore, ya sake fitar da wani bidiyo da ke nuna lokacin da shi da wasu mambobin tawagarsa suka fuskanci hari a garin Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti.
Sowore ya wallafa sabon bidiyon ne a shafinsa na ɗ da aka tantance a ranar Litinin, inda ya nuna damuwarsa kan yadda wasu mutane ke ƙoƙarin rage girman lamarin ta hanyar bayyana shi a matsayin kawai saɓani tsakanin wasu mutane.
Mai fafutukar ya yi zargin cewa harin wani yunƙuri ne na kisan gilla da aka shirya domin hallaka shi.
A cikin saƙon da ya wallafa tare da bidiyon, ya ce: “Wannan wani bidiyo ne na daban da ke nuna mummunan harin da aka kai mini da mambobin tawagarmu a Ado-Ekiti. Abin mamaki ne yadda wani zai kalli wannan tashin hankali ya ce kawai saɓani ne tsakanin wasu mutane. Muna nan daram kan matsayarmu cewa wannan yunƙuri ne na kisan gilla da aka tsara.”
A baya, jaridar NewsRegion ta rawaito cewa an kai wa ɗan takarar shugaban ƙasa na AAC hari ne a Jihar Ekiti yayin ziyarar da ya kai jihar a makon da ya gabata.
Lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda ’yan Nijeriya da dama suka yi Allah-wadai da harin.
Sowore ya dage cewa harin wani yunƙuri ne na kisan gilla da aka shirya domin hallaka shi. Sai dai rundunar ’yan sanda ta bayyana lamarin a matsayin arangama tsakanin Sowore da wasu mutane.
