Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Wata sabuwar doka da Hukumar Sadarwa ta ƙasa (NCC) ta bullo da ita na iya jefa masu harkar kasuwancin wayoyi cikin mawuyacin hali, tare da yin illa ga harkokin kasuwancinsu.
Zaɓaɓɓen shugaban ƙungiyar Association of Mobile Phones and Allied Products Traders of Nigeria (AMPAT) ta ƙasa, reshen Jihar Kano, wanda kuma shi ne zaɓaɓɓen shugaban kasuwar waya ta Farm Centre, Ambasada Jamilu Bala Gama, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai.
A cewarsa, bisa tunaninsu da lissafinsu a matsayinsu na ’yan ƙasa, sabuwar manufar da hukumar ta bullo da ita ba ta zo a lokacin da ya dace ba.
Ya ce duk wata manufa da gwamnati za ta bullo da ita, ya kamata a sanar da ’yan ƙasa tun da wuri, domin su samu damar fahimtarta tare da nemo hanyoyin ɗaukar matakan da ba za su cutar da sana’arsu da kuma al’ummar da suke hulɗa da su ba.
Ambasada Jamilu Bala Gama ya yi kira ga mahukunta da su dakatar da aiwatar da dokar, domin sake duba wa’adin da aka ba wa ’yan kasuwar wayoyi, tare da tabbatar da cewa matakin ba zai kawo cikas ga masu saye da sayar da wayoyi ba.
Ya bayyana cewa, lokacin da NCC ta bullo da dokar, ta ba da ɗan gajeren wa’adi na ƙasa da makonni biyu zuwa wata ɗaya. Ya ce hukumar ta gayyace su ofishinta da ke Kano ne kawai, inda ta yi musu taƙaitaccen bayani cewa dokar za ta fara aiki nan ba da jimawa ba.
Jamilu Bala Gama ya ƙara da cewa sun rubuta wa hukumar NCC wasiƙu daban-daban, inda suka bayyana mata korafe-korafensu da kuma yadda lamarin zai shafe su da sauran al’umma, musamman talakawa da duk masu harkar wayoyi a Nijeriya, kasancewar dokar ta zo musu ba zato ba tsammani.
A ƙarshe, ya ce wannan doka za ta ƙara jefa masu sana’ar wayoyi cikin ƙalubale mai tsanani.
