Gwamnatin Kebbi na godiya ga Tinubu kan ziyara mai tarihi

Spread the love

Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR Birnin Kebbi

Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana matuƙar godiya ga Shugaban Kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu dangane da ziyara mai tarihi wadda ta fi kowace ziyarar wani shugaba ƙasa armashi a tarihin jihar, wadda aka yi ranar Talata.

Da yake ma ‘yan Jarida bayani, kwamishinan watsa labarai da al’adu Yakubu Ahmed Birnin Kebbi, ya ce gwamnati da kuma shugabannin jam’iyyar APC, suna matuƙar farin ciki ga shugaban ƙasa, yadda ya samu lokaci duk da ayyukan tarayyar ƙasa da ke gabanshi, ya zo Kebbi, ya kuma gana da jama’ar jihar a lokacin gangamin yaƙin neman zaɓe na shugaban ƙasa.

Ya ce jihar Kebbi ta wanzar da mubaya’a ga gwamnatin tarayya da nufin kawo ci gaba ga jihar da kuma Najeriya baki- ɗaya.

Yakubu ya ce irin dubban-dubatan jama’a da suka yi dandazo sukayi ma shugaban ƙasa marhabin sannan kuma suka halarci taron yaƙin neman zaɓe da aka gudanar, ya nuna cewar jihar ta amince da shirin Tinubu na sake farfado da Najeriya, (watau, Renewed Hope Agenda) da kuma ƙawance na ci gaba, tsakanin gwamnatin tarayya da kuma gwamnatin Gwamna Nasir Idris.

Kwamishinan ya ce gagarumar nasarar da aka samu na zuwan ziyarar taron gangami na yaƙin neman zaɓe na shugaban ƙasa Kebbi, ƙungiyoyi kamar, ‘ya’yan jam’iyyar APC da kuma shugabannin addini da kuma ‘yan siyasa masu-ruwa-da-tsaki da kuma kungiyoyin mata da kuma ƙungiyoyin matasa da kuma ‘yan kasuwa da kuma kungiyoyin sufuri da kuma sauran al’umma, sun bada irin tasu gudunmawa wurin samun nasarar ziyarar Tinubu.

Yakubu ya ce gwamnati na kuma nuna godiya ga hukumomi da jami’an tsaro da kuma ‘yan Jarida da kuma kwamitocin shirye-shiryen taron, da kuma mutane waɗanda suka sanya hannu a lamarin na ƙashin kansu, da kuma ma’aikatan gwamnati, waɗanda duk gaba ɗayansu suka bada irin tasu gudunmawa wurin samun nasarar ziyarar ta shugaban ƙasa cikin farin ciki da kuma kwanciyar hankali.

By ukarofi

Leave a Reply