2027: Yaƙin basasar cikin gida Tinubu, Atiku da Obi ke yi, inji Sule Lamiɗo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamiɗo ya bayyana takarar shugaban ƙasa da ya haɗa Shugaba Bola Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi a matsayin “yaƙin basasar cikin gida”, inda ya ce baki ɗaya ‘yan siyasa ukun sun haɗu akan tarihin siyasa iri ɗaya.

Lamiɗo, wanda tsohon Ministan Harkokin Wajen Nijeriya ne kuma jigo a jam’iyyar PDP, ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Arise a ranar Alhamis, 19 ga Nuwamba, 2027, yayin bayar da amsa kan damarmakin Tinubu a Arewa gabanin zaɓukan 2027.

Ya ce, yana kallon gwabzawar ta wata fuska, inda ya ce baki ɗaya mutane ukun a lokuta mabambanta ‘yan jam’iyya ɗaya ne ko sun haɗu a inuwar siyasa guda. “Duk mutane uku ko ‘yan takara ukun, Atiku, Tinubu da Peter Obi, sun zo ne daga tarihin siyasar iri ɗaya, dukkan su. A wani lokaci, kun sani, suna ko dai PDP ko APC. Don haka, a wajena kamar wani salo ne na yaƙin basasar cikin gida,” inji Lamiɗo.

Duk da cewa jiga-jigan ‘yan siyasa ukun na jam’iyyun siyasa mabambanta, sun taɓa kasancewa a muhimman ɓangarorin siyasa da sun taimaka wajen inganta Jamhuriyar Nijeriya ta huɗu.

Tinubu, wanda ɗan APC ne a yanzu, ya fara siyasarsa ne a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), gabanin zama jigo a Action Congress of Nigeria (ACN), wadda ta haɗe da wasu jam’iyyu wajen samar da APC a shekarar 2013.

Haka ma Atiku, wanda tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa ne tsakanin 1999 da 2007 a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ya riƙa sauya jam’iyyu a lokuta mabambanta a baya. Ya tsaya takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, kafin daga bisani ya koma ADC gabanin zaɓukan 2027.

Kazalika, Obi, wanda tsohon Gwamnan Jihar Anambara ne a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar All Progressives Grrand Alliance (APGA), ya koma PDP kuma ya yi wa Atiku Abubakar abokin tafiya a zaɓen shugaban ƙasa na 2019. Ya tsaya takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin Labour Party (LP a zaɓen 2023 kafin koma wa jam’iyyar NDC gabanin 2027.

By Babaji

Leave a Reply