Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kungiyar Editoci ta Nijeriya (NGE) ta yi Allah-wadai da kama, tsarewa da gurfanar da ɗan jaridar Foundation for Investigative Journalism (FIJ), Daniel Ojukwu, inda ta buƙaci a sake shi nan take.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar 15 ga Nuwamba, wadda Shugabanta, Eze Anaba, da Babban Sakataren ƙungiyar, Onuoha Ukeh, suka sanya wa hannu, ƙungiyar ta kuma buƙaci a sake duba tuhume-tuhumen da aka shigar a kan Ojukwu da wanda ya kafa FIJ, Fisayo Soyombo.
NGE ta ce ta damu matuƙa da yadda ake gurfanar da Ojukwu bisa rahotannin da ya wallafa waɗanda suka yi tambayoyi kan yadda Ofishin Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban ƙasa kan Manufofin Cigaba Mai ɗorewa (SDGs) yake kashe kuɗaɗen gwamnati.
A halin yanzu, ana tsare da Ojukwu a gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja, bayan gurfanar da shi a gaban kotu kan tuhume-tuhume 12 da suka shafi zargin cin zarafi ta intanet da ɓata suna ta hanyar aikata laifi.
A cewar NGE, binciken ɗan jaridar ya gano zargin biyan sama da naira miliyan 147, kwatankwacin dala 109,000, ga wani gidan cin abinci da ke Abuja domin gina azuzuwa da cibiyar koyon sana’o’i a wata makarantar firamare da ke Legas.
ƙungiyar ta ce rahoton ya haifar da tambayoyi masu muhimmanci kan ko waɗannan ayyuka sun wanzu da kuma ƙwarewar kamfanin da aka bai wa kwangilar. Ta bayyana cewa waɗannan batutuwa sun shafi sahihiyar tambayar yadda ake gudanar da harkokin kuɗaɗen jama’a, don haka ya kamata a ba da amsoshi a fili maimakon gurfanar da ɗan jaridar.
NGE ta kuma nuna damuwa kan yadda aka tsare Ojukwu duk da cewa ya musanta aikata laifukan da ake zarginsa da su. Ta ce an ɗage sauraron buƙatarsa ta neman beli, wanda aka tsara yi a ranar 12 ga Nuwamba, zuwa ranar 1 ga Disamba.
ƙungiyar ta ce amfani da kama mutum, tsare shi da kuma tuhume-tuhumen laifi saboda aikin jarida yana jefa shakku kan jajircewar hukumomi wajen kare ‘yancin aikin jarida, ‘yancin faɗin albarkacin baki da kuma haƙƙin samun bayanai da Kundin Tsarin Mulkin ƙasa ya tanada.
NGE ta sake jaddada matsayarta na adawa da amfani da dokokin yaƙi da laifukan intanet da jami’an tsaro ke yi wajen gallaza wa ‘yan jarida.
“Binciken aikin jarida ba laifi ba ne. Yin tambayoyi kan yadda ake kashe kuɗaɗen gwamnati ba cin zarafi ta intanet ba ne. Neman jami’an gwamnati su yi bayani kan yadda suke gudanar da ayyukansu ba ɓata suna ba ne,” inji ƙungiyar.
Ta ce dole ne masu riƙe da muƙaman gwamnati su kasance a shirye domin a riƙa bincikar yadda suke sarrafa dukiyar jama’a, kuma bai kamata a kama ko a daure ‘yan jarida saboda rahotannin da suka wallafa kan zargin rashin bin ƙa’ida ba.
Duk da cewa ƙungiyar ta amince cewa mutanen da suka ga an ɓata musu suna suna da damar neman hakkinsu ta hanyar doka, ta yi gargaɗin cewa bai kamata a yi amfani da wannan haƙƙi a matsayin makamin tsoratar da ‘yan jarida ko dakile bincikensu ba.
Ta kuma yi gargaɗin cewa ci gaba da tsare Ojukwu na iya sa ‘yan jarida su ji tsoron gudanar da bincike da wallafa rahotanni masu zurfi.
NGE ta yi nuni da Sashe na 39 da na 22 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999, waɗanda suka tanadi ‘yancin faɗin albarkacin baki da kuma rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen sanya gwamnati a cikin tsarin yin bincike da riƙon amana.
Saboda haka, ƙungiyar ta buƙaci a bayar da belin Ojukwu nan take har zuwa lokacin da kotu za ta yanke hukunci kan tuhume-tuhumen da ake yi masa, a kawo ƙarshen cin zarafin ‘yan jarida, sannan a gudanar da bincike a bayyane kan zargin karkatar da kuɗaɗen gwamnati.
Ta kuma yi kira ga ‘yan sanda da sauran hukumomin gwamnati da su daina amfani da dokokin tsaron intanet wajen warware saɓani da ya taso sakamakon sahihin aikin jarida. Haka kuma, ta buƙaci ɓangaren shari’a da ya tabbatar ba a amfani da tsarin shari’a wajen murƙushe masu sukar gwamnati.
“ƙungiyar ba za ta zura ido ana lalata ‘yancin ‘yan jarida ta hanyar tsoratarwa, cin zarafi da kuma amfani da tsarin shari’ar laifuka ta hanyar da ba ta dace ba,” inji sanarwar.
