Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sanda (PSC) da Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya (NPF) na gudanar da bincike kan kwamishinonin ’yan sanda shida da ke kan aiki bisa zargin samun saɓani a bayanan shekarun haihuwarsu, bayan wata umarni da ta buƙaci jami’an da suka kai shekarun ritaya na 60 da su bar aiki.
Wannan lamari ya haifar da tambayoyi kan sahihancin bayanan ma’aikata a cikin rundunar ’yan sanda, musamman zargin cewa wasu manyan jami’ai na iya sauya shekarun haihuwarsu domin tsawaita lokacin da za su ci gaba da aiki.
Rikicin ya biyo bayan wata sanarwa ta cikin gida da rundunar ’yan sanda ta fitar, wadda ta umarci kwamishinonin da abin ya shafa da su gabatar da sanarwar ritayarsu bayan sun kai shekarun ritaya na dole, wato 60.
Sanarwar mai taken “Discharge and Retirement” tana ɗauke da lambar INGENPOL/FORSEC Abuja – DTO 020749/11/2026, kuma an ce an aika kwafinta ga jami’an da abin ya shafa, Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sanda, Sashen Kuɗi da Asusun Rundunar, Kwamandan Shiyya ta 7, Kwalejin ’Yan Sanda, makarantun horas da ’yan sanda da sauran sassan da abin ya shafa.
Wannan mataki ya biyo bayan rahotannin cewa jami’an da abin ya shafa sun ƙi yin ritaya bisa ƙa’idojin aikin gwamnati, inda ake zargin wasu daga cikinsu sun nemi samun ƙarin girma zuwa muƙamin mataimakan sufeto-janar na ’yan sanda (AIG).
An tattaro cewa an gano saɓanin da ke cikin bayanan ma’aikatan ne bayan wani mai fallasa bayanai ya miƙa bayani ga Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sanda.
Rahoton ya bayyana sunayen jami’an da abin ya shafa da cewa su ne CP Adamu A. Elleman, CP Abdullateef A. Yusuf, CP Lasisi A. Titilola, CP Markus Ishaku Basiran, CP Ajayi Oluyemi da CP Sylvester Onyie Uzoefuna.
An zargi cewa saɓanin da aka samu a bayanan ma’aikatan ya shafi sauya shekarun haihuwa, wanda ya ba wasu daga cikin jami’an damar ci gaba da aiki bayan wa’adin ritayarsu na doka.
Bisa bayanan da aka samu, shugaban hukumar PSC, DIG Hashimu Salihu Argungu (mai ritaya), ne ya ƙaddamar da binciken bayan samun bayanan daga mai fallasa sirri, kuma rahotanni sun nuna cewa binciken ya tabbatar da wasu daga cikin zarge-zargen, lamarin da ya jawo fitar da umarnin yin ritaya.
Rahoton ya ƙara da cewa jami’an da abin ya shafa na da ranakun ritaya daban-daban bisa ga shekarun haihuwarsu, inda ake zargin wasu sun riga sun wuce shekarun ritaya da shekaru da dama.
Sai dai bayanan da jaridu daban-daban suka wallafa sun nuna akwai saɓani a sunaye da ranakun haihuwa da aka bayyana a cikin rahotannin wasiƙar cikin gida ta rundunar ’yan sanda, lamarin da ya sa ake buƙatar tantance sahihancin bayanan ma’aikatan da kansu.
Jaridar Saturday Tribune, a rahotonta na ranar 7 ga Nuwamba, ta ce sanarwar rundunar ta ambaci jami’ai shida, amma ta ƙunshi sunaye biyar ne kawai, tare da ranakun haihuwa guda shida.
Wannan lamari ya sake dawo da batun sa ido kan ƙa’idojin ritaya da yadda ake kula da bayanan ma’aikata a cikin Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya.
Shekarun ritaya na 60 na ci gaba da kasancewa muhimmin sharadi da ke jagorantar ritayar ma’aikatan gwamnati, tare da wasu ƙa’idojin tsawon lokacin aiki da suka dace.
Sabon ci gaban ya haifar da tambayoyi kan ingancin tsarin tantance bayanan ma’aikata a rundunar da kuma irin tasirin da ake zargin waɗannan kura-kurai suka yi kan ƙarin girma da tsarin maye gurbin manyan jami’ai.
Idan aka tabbatar da zarge-zargen, lamarin na iya shafar amincin tsarin ƙarin girma da ritaya a rundunar ’yan sanda, musamman idan aka gano cewa wasu jami’ai sun amfana da bayanan ma’aikata marasa inganci.
Ya zuwa lokacin kammala rahoton, babu wata cikakkiyar sanarwa da aka fitar a bainar jama’a daga PSC ko Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya da ke bayyana sakamakon binciken, hujjojin da aka tattara ko kuma matakin ƙarshe da aka ɗauka kan jami’an da abin ya shafa.
Ana sa ran hukumar da rundunar za su yi karin haske kan saɓanin da aka samu tare da bayyana duk wani matakin ladabtarwa ko na gudanarwa da zai biyo bayan binciken.
Ko da yake ba a samu damar tuntuɓar kakakin hukumar, Mista Torty, domin samun cikakken bayani kan binciken ba, wani jami’in hukumar ya tabbatar da faruwar lamarin.
