Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Jihar Legas ta bayyana aniyarta ta ƙara samar da megawatt 2,000 na wutar lantarki zuwa watan Maris na shekarar 2027, domin biyan buƙatun makamashi da ke ƙaruwa tare da inganta samar da wutar lantarki a jihar.
Kwamishinan Makamashi da Albarkatun Ma’adinai na jihar, Biodun Ogunleye, ne ya bayyana wannan buri a taron ƙoli kan makamashi na Legas na shekarar 2026 (Lagos Energy Summit 2026), wanda aka gudanar ƙarƙashin taken: “Sauyin Fasalin Makamashi a Legas: Sauya Makomar Makamashi.”
Ogunleye ya ce, shirin ya ƙunshi zuba jari a fannoni uku na samar da wutar lantarki, wato samarwa, isarwa da kuma rarrabawa, domin rage giɓin da ke tsakanin yawan wutar da ake samarwa da kuma buƙatar da ake da ita, tare da gina ingantaccen tsarin kasuwar wutar lantarki a jihar. Ya bayyana cewa, sauye-sauyen da ake shirin aiwatarwa ba su taƙaita ga ƙara yawan wutar da ake samarwa kawai ba ne, a’a, sun haɗa da tabbatar da wadatar makamashi, ƙarfafa hanyoyin rarraba wutar lantarki da kuma rage matsalar ƙarancin makamashi da ke addabar al’umma.
Kwamishinan ya ce, gwamnatin jihar tana tattaunawa da wasu masu zuba jari guda 22 domin kammala yarjejeniyoyin zuba jari a ɓangaren makamashi. Ya kuma bayyana cewa ana ƙoƙarin warware matsalolin da suka rage dangane da yarjejeniyoyin saye da sayar da wutar lantarki (Power Purchase Agreements) tsakanin gwamnatin jihar da Gwamnatin Tarayya. Ogunleye ya nuna kyakkyawan fata cewa warware matsalolin kwangiloli da na zuba jari da suka dabaibaye ɓangaren zai taimaka wajen inganta samar da wutar lantarki.
Haka kuma, ya jaddada muhimmancin amfani da hanyoyin samar da makamashi masu sabuntawa, kamar hasken rana, iska da makamashin ruwa. Ya buƙaci mazauna jihar da masu gudanar da harkokin kasuwanci da su rungumi waɗannan hanyoyin samar da makamashi a matsayin madadin wutar lantarki, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ƙarfafa babbar hanyar samar da wutar lantarki ta ƙasa.
