Kwamishinan yaɗa labarai na Kebbi ya ce ana yi masa barazana

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Kwamishinan yaɗa labarai da al’adu na Jihar Kebbi Alhaji Yakubu Ahmed Birnin Kebbi ya bayyana cewa waɗansu da bai san ko su wanene ba suna yi masa barazanar kashe shi ko kuma sace shi da iyalan sa.

Kwamishinan ya rubuta ƙorafi ga hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) kan zargin yunƙurin wasu mutane da ba a san su ba na sace shi da iyalansa a Birnin Kebbi.

Ƙorafin, wanda aka rubuta a ranar 15 ga Nuwamba, 2026, an aike shi ga darakta janar na DSS ta hannun mataimakin darakta janar mai kula da ayyuka na jihar Kebbi.

Ya kuma aika kwafin ƙorafin ga babban sufeton ‘yan sanda na ƙasa da kuma kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kebbi.

Takardar ta bayyana cewa ya fara fahimtar lamarin inda daga farko a ranar 10 ga Nuwamba, lokacin da shi da matarsa ke yin motsa jiki na safiya kamar yadda suka saba, a kan titin Sani Abacha Bypass.

Ya yi zargin cewa wata mota ƙirar van mai farin launi, mai gilashin duhu-duhu gaba ɗaya, mai lambar Agege mai jan launi ta biyo ta aron hannu ta rage gudu kusa da su, ta kuma yi kamar za ta bude daya daga cikin kofofinta. Ya ce ya kuma ga abin da ya yi kama da bakin bindiga.

Kwamishinan ya ce shi da matarsa sun gudu zuwa wani plaza da ke kusa don tsira, bayan sun yi zargin cewa mutanen da ke cikin motar suna binsu.

Ya ce wani jami’in tsaro da ke aiki a gidan gwamnati, wanda ya kira don neman taimako, ya iso nan take, lamarin da ya tilasta motar ta gudu da sauri.

Ƙorafin ya kuma yi zargin cewa an sake ganin motar nan a kusa da gidansa na biyu da ke Bayan Oando tsakanin karfe 6:30 zuwa 7:00 na safe a ranar 15 ga Nuwamba, inda aka ce ta tsaya kimanin minti biyar kafin ta tafi.

Da yake neman a gaggauta bincike, kwamishinan ya nemi a tura jami’an tsaro na farin kaya na wucin gadi don kare iyalansa, da kuma sa ido kan motar da ake zargi, da kuma sanya ido kan wasu sassan titin Sani Abacha Bypass, musamman tsakanin karfe 6 na safe zuwa 7 na safe. Ya nemi a ɗauki matakan kariya don gano waɗanda ke bayan yunƙurin cutar da shi da iyalansa.

By ukarofi

Leave a Reply