Daga AISHA ASAS
Bayan shafe kusan sa’o’i 17 a hannun masu garkuwa da mutane, dukkan mutanen da aka riƙe a wani babban kanti da ke birnin Cartagena na ƙasar Colombia sun samu ‘yanci, bayan jami’an tsaro sun kai farmaki kan ginin da aka tsare su.
Lamarin ya faru ne a ranar Talata, inda wasu mutane ɗauke da makamai suka kutsa cikin babban kantin, tare da yin garkuwa da mutane 30 da suka haɗa da ma’aikata da kwastomomi.
Rahoton jaridar The Guardian na ranar 25 ga Nuwamba ya bayyana cewa jami’an tsaro sun gudanar da aikin ceto ne bayan tattaunawar da aka yi da masu garkuwar ta ci tura.
Wasu daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su sun samu ‘yanci tun kafin jami’an tsaro su kai farmakin ƙarshe, inda aka ceto sauran mutum 20 da misalin ƙarfe 1:30 na dare, bayan shafe tsawon lokaci a hannun masu garkuwar.
A yayin aikin, jami’an runduna ta musamman sun kutsa cikin ginin ta hanyar amfani da wasu ƙofofin shiga da aka toshe, tare da amfani da na’urorin tayar da hayaniya domin rikita masu garkuwar.
Rahoton ya ce mutum ɗaya daga cikin masu garkuwar ya mutu yayin farmakin, yayin da aka kama wasu huɗu.
Shugaban ƙasar, Abelardo de la Espriella, ya je birnin Cartagena domin bibiyar yadda aikin ceto ke gudana. Ya bayyana cewa jami’an tsaro sun yi amfani da damar da aka ba masu garkuwar na su miƙa wuya tare da sakin mutanen, amma suka ƙi.
An ce masu garkuwar sun shiga babban kantin ne bayan wani yunƙurin satar kuɗi daga motar da ke jigilar kuɗaɗe ya ci tura, inda jami’an tsaro suka fara bin sawunsu.
Wannan lamari ya zo ne a lokacin da Colombia ke fuskantar matsalolin tsaro da suka haɗa da hare-haren ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, satar mutane da kuma hare-haren bama-bamai a wasu sassan ƙasar.
Duk da cewa an samu nasarar kuɓutar da mutanen, lamarin ya sake jawo hankalin jama’a kan buƙatar ƙarfafa tsaro a wuraren da jama’a ke taruwa domin gudanar da harkokinsu na yau da kullum.
