Daga IBRAHIM SHEME
Ibrahim Malumfashi ne ya ƙirƙiro kalmar “Adabin Kasuwar Kano”, wanda da yawan marubuta da manazarta (ciki har da ni) su ka ɗauka ƙasƙantarwa ce. Mun shafe shekaru mu na yaƙi da Farfesa Malumfashi kan wannan kalmar, kafin kowannen mu ya aje makamin sa (wato biro) a gefe ɗaya, domin duk abin da za a ce, an ce, kuma duk abin da za a yi, an yi.
Na jima ina tunanin waɗanne ne alamomin littafin irin wannan adabin? To, bayan na gama tunani na, a cikin 2014 na lissafa su. Wani abu da na gano shi ne yawancin alamomin adabin kasuwar Kano akwai su a finafinan Hausa, to amma ‘yan fim sun fi marubuta ɗaukar aikin su a matsayin sana’a, kuma sun fi cin moriyar gumin su.
Ga yawanci kuma manyan alamomin:
1. Littafin na Hausa ne ko na Turanci. Kuskure ne a ɗauka cewa sai littafin Hausa ne kan faɗa a farfajiyar wannan kalma. To amma na Hausan sun fi yawa.
2. Marubuci kan ɗauki nauyin buga littafin shi, ba kamfani ba. A ƙa’idar wallafa, marubuci daban, mawallafi daban. Mawallafi ne ke da kamfanin wallafa littattafai, kuma ɗan kasuwa ne. Amma a da’irar adabin kasuwar Kano, marubuci ya kan kasance shi ne ke da kamfanin wallafar, kuma ko da zai buga littafin wani marubucin to sai dai shi wancan marubucin ya biya kuɗin.
3. Babu lambar ISBN a yawancin littattafan. To amma ko da an sa lambar, littafi zai iya kasancewa cikin da’irar adabin saboda wasu abubuwan.
4. Babu kyakkyawan nahawu. Saboda haka za a ga ɗimbin kurakurai a littafin, daga raba kalma ko haɗa kalma har zuwa bin ƙa’idojin rubutu kamar su saka aya, dakatau, waƙafi, alamar motsin rai, ayar tambaya, alamomin fara magana da rufe ta, ds. Kai, hatta sunayen mutane da na garuruwa akwai waɗanda ba daidai ba a littafin.
5. Marubuci bai bayar da littafi wani masani ya gyara masa kafin a buga. Gyara ya haɗa da nahawu da kuma sukar labarin. Wani marubucin ya na tsoron kada ya ba ɗan’uwan sa marubuci a sace masa labari, domin an sha yi! Da ya gama rubutawa sai ya kai wurin ɗab’i kai-tsaye.
6. Rarraba littafi zuwa kashi na 2, 3, 4 ko ma fiye. Ana yin haka domin riba, kuma domin masu karatu kan dinga tambayar ina na 2 ko ina na 3. Abin mamaki, masu karatu ba su cewa ina na biyun ‘Ganɗoki,’ ‘ƙarshen Alewa ƙasa,’ ‘Mace Mutum’ ko ”Yartsana.’ Dalili shi ne sun san labarin ya ƙare, ko kuma su na ganin waɗannan marubutan ba masu karkasa labari ba ne.
7. Saka lambar wayar marubuci ko adireshin i-mel, wasu ma har da BB Pin ko lambar gida, a cikin littafi, saboda masu karatu su bugo waya su faɗi ra’ayin su kan littafin, kuma su kambama marubuci. Ta wannan hanyar, wasu matan aure marubuta sun sha samun ƙalubale daga mazajen su.
8. ƙulla hulɗar abota ko zumunci tsakanin marubuci da mai karatu har ta kai ga ana ziyartar juna, ko ka ga yarinya ta sauka a gidan marubuciya wai ta na neman shawara kan wani abu (misali aure). Wani matashin marubucin ma kan samu ƙulla soyayya da mace ta wannan hanyar.
9. Duk tunanin marubuci game da kasuwancin littafi bai wuce garin Kano. A nan manyan dillalan littafi su ke. Marubuci bai tunanin ya kai littafin sa Kaduna ko Abuja ko Sakkwato; ya dogara kan dillali ya yi masa wannan, ko kuma dillalan da ke can su zo Kano su saya su tafi. Sannan marubuci ya na kallon kasuwar Sabon Garin Kano ko bakin Bata nan ne cibiyar sayar da littafin sa.
10. Yawaitar ƙungiyoyin marubuta, kuma da yawa ba su jituwa da juna.
11. Rashin ingancin littafi wajen tsara shafukan sa, da takarda, da ɗab’i (a Turance, “final finishing”).
12. Doguwar sadaukarwa a littafi, tare da godiya ga miji ko mata ko ‘yan’uwa da masoya da makaranta da ‘ya’ya.
13. Rige-rigen fito da littafi a tsakanin marubuta, wanda gasa ko gaba ke haifarwa. A mako ɗaya sai littafi biyar su fito.
14. Maimaita labarin wani littafin ta hanyar sauya masa siga. Wani lokaci ma labarin wani marubucin za a sata a sauya masa fasali a yi littafi.
15. Rashin shirya babbar gasa ta rubutu, ko baje kolin littattafai.
16. Kwaikwayon yadda wani ya yi nasa labarin ta fuskar tsarin da ya bi, maimakon marubucin ya fito da nasa.
17. Samun marubuta ‘yan kasuwa, waɗanda ke da “kamfanonin” buga wa sauran marubuta littafi, wata sa’a har da tallata masu littafin. Wata sa’a kashe-mu-raba su ke yi wajen buga littafin.
18. Juya labarin fim ɗin Indiya ko na Turawa ko na Canis ko na Larabawa zuwa littafi.
19. Rige-rigen rubuta labari a Facebook ko guruf ɗin WhatsApp. Tsarin wannan shi ne sai a fara labari ko da shedara ɗaya ce, sai kuma a bari sai ‘yan guruf sun faɗi ra’ayin su sannan a ci gaba. Sau da yawa ma babu labarin a aje, a lokacin ne ake rubuta shi, kuma ra’ayoyin ’yan guruf ɗin ya kan ja akalar marubucin.
20. Rashin ƙoƙarin a fassara littafi zuwa wasu harsunan na duniya wanda ba su jin Hausa, kamar yadda aka yi wa ‘Alhaki Kwikuyo’ na Balaraba Ramat Yakubu.
21. Rashin damuwar gwamnati ga harkar rubutun littafi. Gwamnati ta fi damuwa da ‘yan fim, shi ya sa ta kafa masu hukuma, kuma ta na shirya masu bitoci da bukukuwan baje kolin finafinai. Bugu da ƙari, ofisoshin jakadun ƙasashen waje da ƙungiyoyi masu zaman kan su (NGOs) kan kira ‘yan fim su ba su tallafi, ciki har da kai su ƙasashen su domin su ƙara wayewa kan harkar. A lura, marubutan Ingilishi ma kan samu wannan tagomashin. Marubutan Hausa kuwa ko oho!
22. Rashin zurfin hikima wajen bada labari, wajen wasa da harshe ko sarƙaƙiyar labari.
23. Shaida wa mai karatu a cikin littafi cewa ana nan ana aiki kan wani littafin wanda zai fito nan gaba, ko kuma bada haƙuri kan wani littafi ko rashin amsa waya, ds.
24. Yawanci jigon littafi bai wuce soyayyar matasa ko matsalar aure ko kasuwanci.
25. Saka Ingilishi a cikin labari, ba don ya zama tilas ba sai don a burge mai karatu.
26. Yawanci mata ne ke yin rubutun. Kai, har ta kai maza kan yi rubutu da sunan mace don kiran kasuwa. An ce masu karatu sun fi karanta littattafan mata.
27. Saka hoton kyakkyawar fuskar mace a bangon littafi. Har hotunan matan Indiya da Larabawa da Turawa ake ɗaukowa daga intanet a saka; wasu har hijabi ake yi masu ta hanyar Photoshop. Wannan kan nuna kamar Bahaushe bai da mummunar mace ko tsaka-tsaki. Wani lokaci kuma hoton katafaren gida ake ɗaukowa daga intanet ɗin ana makawa.
28. Ba a cika bada labarin talakawa ba, sai ‘yan boko da manyan ‘yan kasuwa. Ko da labarin talaka aka faro, to sai ya rikiɗe ya zama na masu kuɗi, masu fita zuwa ƙasar waje ko masu babbar harka.
29. Idan za a nuna an fita waje a labari, to tafiyar ba ta wuce Ingila, Amerika, Saudiyya, Dubai ko Indiya.
30. Sayar da littafi ɗungurungum ga ɗan kasuwa, shi ya buga ya samu kuɗi. Yawanci babu rubutacciyar yarjejeniya ta wannan cinikin.
31. Amsar kwangilar rubuta littafi daga wurin ɗan kasuwa. “Nawa zan ba ki, ki rubuta mani littafi mai shafi saba’in?” Idan ta rubuta ta ba shi, sai ya saka sunan da ya ga dama, amma idan fitacciyar marubuciya ce, to sai ya bar sunan domin za a fi saye. Idan namiji ne ya yi rubutun, to za a iya ƙirƙirar sunan mace a saka.
32. Gamewar marubuta biyu ko uku su yi littafi guda ɗaya. Idan sun ga dama, su sa sunayen su, idan ba su ga dama ba su sa sunan mutum ɗaya.
33. Rashin daɗewar littafi a kasuwa. Idan littafi ya ci kasuwa wata shida, shi kenan ba ka ƙara jin ɗuriyar sa. A lura, har yanzu ana buga ‘Ganɗoki,’ wanda ya fara fitowa a 1934.
34. Da wuya ka ga an yi sharhi kan littafin a wata jarida ko mujalla, duk da yake akwai jaridun Hausa da yawa.
35. Kafafen yaɗa labarai sun fi damuwa da rayuwar ‘yan fim. Misali, idan Fauziyya D. Sulaiman ta haihu, ba labari ba ne, to amma idan Muhibbat Abdussalam ta haihu, labari ne da dukkan jaridu da mujallun Hausa za su buga. Amma a marubutan Turanci na Nijeriya, idan Chimamanda Ngozi Adichie ta yi aure ko ta haihu, babban labari ne!
36. Da wuya ka ga an yi nazarin littafin a matakin digiri ko difiloma, ko a yi ƙasida a kan sa a cikin wata mujalla ta masu bincike, ko a gabatar da lacca a kan sa a wani taro a jami’a ko babbar makaranta.
37. Da wuya ka ga an yi littafin nazari kan marubucin wannan adabin. Ya zuwa wannan lokacin babu wani marubuci adabin kasuwar Kano da aka yi littafi a kan sa. Amma an yi littattafai kan B.M. Dzukogi, wanda matashin marubucin Turanci ne.
38. Saurin shuɗewar zamanin marubuci, har ka ji an daina maganar sa, sai ta wanda ake yayi a yanzu. Misali, ɗan’azimi Baba, Bilkisu Salisu Ahmed Funtua, Ado Gidan Dabino, duk ba a maganar su duk da yake yawan littafin da kowannen su ya buga ya fi na marubucin Turancin nan marigayi Abubakar Gimba (wanda har yanzu ana maganar sa).
39. Kallon rainin da ake wa littattafan wannan adabi ya shafi dukkan littattfan Hausa, ya sa a yau ko da wani ya yi littafi mai inganci sai a jefa shi cikin kwandon sharar irin waɗannan littattafan, ko da kuwa ba ma na adabin ba ne.
40. Ana kallon marubuci kusan ɗaya da ɗan fim ta fuskar darajar su. Wasu ma sun fi ganin girman mai yin fim.
Waɗannan hujjojin sun taimaka wajen bunƙasar ”adabin kasuwar Kano,” to amma kuma su na taimakawa gaya wajen dakusar da ci-gaban adabin Hausa na sashen rubutun littafi.
