
Daga BELLO A. BABAJI
Rundunar ƴan sanda a Jihar Gombe, ta ce ta kama wani uba ďan shekara 47 bisa zargin sa da yi wa agolan da ke gidansa mai shekaru biyu fyaďe.
Kakakinta, DSP Buhari Abdullahi ya faďi hakan a wata takarda, ranar Talata.
Ya ce, lamarin ya auku ne a ranar 5 ga watan Mayu a yankin Rukunin gidaje na Shamaki dake Tudun-Wada a garin Gombe, inda aka kama wani Mohammed Magaji bayan sanarwa ga ƴan sanda daga matarsa.
Matar, mai suna Hauwa’u Usman ta ce a safiyar ranar 5 ga watan Mayu ne mijin nata ya ďauki agolar cikin sirri zuwa wani ďaki, inda ya yi lalata da ita.
Samun labarin ke da wuya rundunar ta aika wata tawaga, lamarin da ya yi sanadin kamo wanda ake zargin da yarinyar tare da kai su wani asibiti cikin gaggawa don tabbatar da hakikanin al’amarin.
DSP Abdullahi ya kuma ce, za a mika su zuwa ga kotu da zarar an kammala bincike akan lamarin.
A Karamar Hukumar Billiri dake jihar kuwa, ƴan sanda sun kama wani Isah Adamu mai shekaru 35 a yankin Rukunin Gidaje na Golkos bisa zargin lalata da ƴar shekara shida.
A ranar 5 ga Mayu ne aka ruwaito wanda ake zargin ya kai yarinyar wani gida dake Rukunin gadaje na Awai, inda ya yi lalata da ita ta hanyar nuna mata karfi.
Lamarin da mahaifiyarta ta sanar da ƴan sanda a kai, wanda ya sa aka gaggauta kamo wanda ake zargin.
Tuni aka garzaya da mai laifin da yarinyar zuwa Babban Asibitin Kaltungo.
Har’ilyau, kakakin ƴan sandan ya ce an kama karin wasu mutane 18 da ake zargi da hannu a manyan laifuka a jihar a makonnin da suka gabata.
