Babu ja da baya har sai Nijeriya ta samu tsaro, inji shugaban sojojin sama

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaban Rundunar Sojojin Sama na Nijeriya (CAS), Air Marshal Hasan Bala Abubakar ya zaburar da jami’ansu bisa kokarinsu na dakile ayyukan ta’addanci a ƙasar, ya na mai cewa babu ja da baya har sai an samu cikakken tsaro ga ƙasa.

Ya bada umarni ne a lokacin da ya ziyarci jami’an a Jihar Katsina inda ya karfafa wa sojojin a yunķurinsu na kawo karshen ta’addanci da suka hada da ƴan bindiga da barayin daji da sauran su.

A lokacin da ya ke jawabi ga sojojin a bikin cikar NAF shekaru 61 da kafuwa, Air Marshal Abubakar ya bayyana cewa an samu ci-gaba a bangarorin atisaye da dama, saidai duk da haka har yanzu akwai sauran aiki a gabansu.

Ya ce, duk da cewa dakarun sun samu nasarori da dama, hakan ba dalili bane na su ajiye makamansu.

CAS’n ya kuma kiraye su da su kara kaimi wajen kai hare-hare akan sansanonin ƴan ta’adda domin kawo karshen ayyukansu a shiyyar Arewa masu Gabas.

Kazalika, ya tunatar da su cewa kwarin-gwiwar ƴan Nijeriya ya dogara ne akan su musamman ayyukansu na sama, don haka wajibi ne su yi nasara akan ƴan ta’adda domin dawo da zaman lafiya mai dorewa acikin al’umma.

By Babaji