Shettima ya buƙaci bankin Musulunci ya zuba jari a Nijeriya

Spread the love

Gwamnatin Nijeriya ta buƙaci bankin Musulunci da ya ƙara zuba jari a kasuwar abincin halal Nijeriya.

Mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima ne ya bayyana buƙatar a yayin da ya yi wata ganawa da tawagar bankin a fadar Shugaban Ƙasa.

Mataimakin shugaban yayi nuni da yadda Najeriya ta sami bunƙasa a harkokin kasuwanci a ƙarƙashin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da irin ƙoƙarin da gwamnati ke yi na magance ƙalubalen da ake fuskanta a muhimman ɓangarorin tattalin arziki da suka haɗar da zuba jari akan ƴan Ƙasa da samar da abinci mai gina jiki, da bunƙasa noma, da kiwon lafiya, da ilimi, da kasuwanci na zamani inda ya ƙarfafa wa bankin gwiwar kan yin amfani da yanayin da ake ciki a matsayin lokaci mafi dacewa na zuba jari a Najeriya, yana mai nuni da sauye-sauye a sassa masu mahimmanci da gwamnatin ta samar.

Baya da bunƙasa tattalin arzikin halal, Kashim Shettima ya buƙaci bankin da ya inganta kasuwanci a ɓangaren fasahar zamani, da hada-hadar kuɗi da sabon shirin Agro-Processing Zones (SAPZ) na samar da muhalli na musamman ga noma da ilmi da ababen more rayuwa da kiwon lafiya.

Ita ma tawagar bankin Musulunci, ƙarƙashin jagorancin Mista Hammad Hundal, ta nuna gamsuwarta da tsare-tsaren gwamnatin shugaba Tinubu inda ta bayyana ƙudurin ta na fifita ƙudurorin Shugaban a matsayin hanyar haɓaka farfado da walwala da magance talauci, da kuma haifar da ci gaban tattalin arzikin.

By ukarofi