
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon mataimaki ga shugaban ƙasa kuma Shugaban Kungiyar Grassroots Initiative Concept, Alwan Hassan ya shaƙi iskar ƴanci bayan shafe sa’o’i a hannun hukumar ƴan sanda da ke sashen binciken manyan laifuka (FCID) a Abuja.
Wata majiya daga gidan su Hassan ta shaida wa manema labarai an sako shi ne da tsakiyar dare a ranar Asabar bayan samun matsi daga makusantansa da magoya baya kan rashin sanin inda aka dosa akan al’amarinsa.
An tsare shi me a lokacin da ya amsa gayyatar FCID a ranar Juma’a.
Duk da cewa rundunar ƴan sanda ba ta fitar da wani rahoto akan lamarin ba, ana tsare shi bai rasa nasaba da zargin da Hassan ya yi akan wasu jiga-jigan Majalisar Dokoki ta Ƙasa.
Tun a farkon makonni da ya gabata ne ya zargi Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin da Haan tantance Abdullahi Garba a matsayin shugaban Hukumar Kula da Wutar Lantarki (NERC).
Alwan Hassan ya yu zargin cewa jagorancin Majalisar na ƙoƙarin siyasantar da al’amarin naɗin Garba a shugabancin NERC.
Haka kuma, ya zargi mambobin majalisar da neman a biya su cin hancin Dala miliyan 10 daga ɓangaren waɗanda aka miƙa sunayensu a muƙamin NERC, ikirarin da ya haddasa cecekuce acikin al’umma.
Tuni majalisar ta ƙaryata zarge-zargen inda ta bayyana su a matsayin ƙarya da ɓatanci da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da jama’a.
