
A daren Asabar wayewar Lahadi a birnin Ibadan, jam’iyyar PDP ta tabbatar da tsohon Ministan Ayyuka na Musamman, Kabiru Tanimu Turaki (SAN), a matsayin sabon shugabanta na ƙasa bayan ya samu rinjayen ƙuri’u a babban taron zaɓen jam’iyyar.
Turaki, wanda ya yi aiki a gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya kasance daya daga cikin manyan ‘yan takarar da aka fi hasashe tun bayan goyon bayan da ya samu daga yawancin shugabannin jam’iyyar daga Arewa kafin taron.
A sakamakon zaben da aka gudanar a gaban wakilai daga sassan kasar, Turaki ya samu kuri’u 1,516, yayin da abokin takararsa, Senator Shehu Lado, ya samu kuri’u 275. Wannan ne ya tabbatar da karbuwarsa a matsayin sabon jagoran jam’iyyar a matakin kasa.
Taron dai ya samu tsaiko, kasancewar PDP ta kori wasu jiga-jigan jam’iyya, ciki har da Nyesom Wike da Ayo Fayose, bisa zargin ayyukan cin amanar jam’iyya. Saidai hakan bai hana sanar da nasarar Turaki ba.
Da yake jawabi bayan nasarar, Turaki ya yi alkawarin farfaɗo da ƙarfin PDP tare da haɗa kan ɓangarorin jam’iyyar, yana mai cewa jam’iyyar za ta sake samun karɓuwa yayin da ake shirin tunkarar zaben 2027 a Nijeriya.
