Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Babban Sakataren Gidauniyar Alhaji Ahmed Ibrahim karfi ya faɗi haka a wajen bikin raba wasu kayan karatu da na gine gine ga wasu makarantun islamiyya da na alumma a jihar.
Ya ce gidauniyar ta kashe waɗannan kuɗaɗe ne ga makarantun boko da na addini tun daga kafuwarta zuwa yau, a ƙarƙashin shirin tallafin ilimi na musamman.
Ibrahim karfi ya bayyana cewa a wannan zangon tallafin na 2025, gidauniyar ta raba littattafan Islamiyya, tabarma (rubber mats), kayayyakin gini da kuma littattafan nuni ga makarantun Islamiyya, Alƙur’ani da na al’umma guda 12 da aka zaɓa daga kowace mazaɓar sanata uku na jihar.
Kayayyakin ginin sun haɗa da buhunan siminti da fenti, rufin bene domin tallafa wa cigaban ilimi a jihar ya ce.
Ya ce kowace mazaɓar sanata, an zaɓi makarantu huɗu da suka ci gajiyar wannan tallafi.
Mazaɓar Katsina;
Makarantun da suka amfana sun haɗa da:
Abdulbaki Tahfizul Qur’an, Madrasatul Islamiyya Baude Makarantar Malam Sani Tokawa, Madrasatul Islamiyya Banye. Dukkaninsu daga ƙananan hukumomin Katsina, Safana, Charanci da Rimi.
Mazabar Funtua kuma sakataren ya bayyana cewa akwai Ɗankwaro Islamiyya Mahuta, Madrasatul Nurul Huda Danjanku,
Madrasatul Raudatul Islam,Ma’arufatul Dinil Islam a ƙananan hukumomin Ƙafur, Ƙanƙara, Faskari da Bakori.
Mazaɓar Daura kuwa sun haɗa da Arabic Islamiyya School Koza,Madrasatul Umar Bin Khattab Gachi,Nurul Huda Islamiyya Unguwar Marina, dukkan su a ƙananan hukumomin Daura, Mai’adua, Kankia da Mashi.
Ibrahim karfi ya jaddada ƙudirin gidauniyar na cigaba da irin wannan tallafi domin ƙarfafa ilimin addini da na zamani a faɗin Jihar Katsina.
Tsohon babban jojin kotun ƙoli marigayi Muhammadu Bello shine shugaban gidauniyar na farko kafin marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya riƙe.
