
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jami’an Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) sun yi nasarar cafke wani Musa Abubakar da ake zargi da aikin raba wa ƴan ta’adda makamai a Jihar Filato da wasu sassan arewa.
Hakan ya biyo bayan wani sakamakon bincike na sirri da hukumar ta samu, wanda ya kai ga kama shi a ranar 12 ga watan Nuwamba, 2025.
Majiyoyi daga hukumar sun bayyana cewa, wanda ake zargin ya amsa cewa yana da hannu a haɗawa da raba muggan makamai da alburusai ga ƙungiyoyin ƴan ta’adda da ake danganta su da alhakin kai hare-hare a sassan Filato.
A cewar wata takarda daga hukumar, an kama shi ne a masana’antar haɗa makaman nasa da ke yankin Mista Ali a Ƙaramar Hukumar Bassa ta jihar.
Daga cikin ababen da aka samu a wajensa akwai sinadaran haɗa boma-bomai da wasu nau’ukan makamai waɗanda DSS ta ƙwace.
Hakan na zuwa ne jim-kaɗan da kama Abdulazeez Obadaki da fi sani da Bomboy, wanda ya tsere daga kurkukun Kuje na Abuja, sannan kuma shi ne ya kitsa hare-haren cocinan Owo da Deeper life.
Waɗannan nasarori da hukumar take samu wajen daƙile ayyukan ta’addanci ya nuna yadda take aiki tuƙuru akan lamuran da suka shafi wanzar da zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasa.
