
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mai taimaka wa Ministan Abuja Nyesom Wike akan harkokin yaɗa labarai, Lere Olayinka, ya bayyana sallamar mai gidansa da tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose daga jam’iyyar PDP a matsayin abinda ya kira da ‘bikin Disamba a Nuwamba’.
A wata takarda da ya fitar a daren jiya Asabar, Olayinka ya bayyana cewa mambobin jam’iyyar suna taro a Ibadan domin yin biki tun kafin watan Disamba, yana mai cewa za a riƙa ganin tsokaci akan taron a matsayin saƙonnin ruɗar da jama’a.
Ya ce, musamman ana gudanar da taron ne domin walwala da nishaɗin al’umma don haka maganganun da aka yaɗa a wajen ba ababen ɗauka da muhimmanci ba ne.
Da fari an yaɗa rahotannin da ke cewa tsagin PDP ya sanar da korar Wike daga cikin jam’iyyar da Sakatare Samuel Anyanwu da kuma tsohon gwamnan Ekiti Ayo Fayose bisa zargin su da yin ayyukan da suka shafi zagon-ƙasa.
Ƙudirin sallamar ta samu amincewar masu zaɓen ƴan takara a taron, wanda Cif Bode George da ya samar da jam’iyyar ya gabatar, wanda Shugaban jam’iyyar na Jihar Bauchi ya goyi baya.
