Gwamnoni sun tsame hannu a korar Wike da wasu a PDP yayin da INEC ta ƙaurace wa taron jam’iyyar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babban taron jam’iyyar PDP ka iya fuskantar ƙalubale duba da cewa babu wakilci na musamman daga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC).

An gano haka ne a lokacin da Gwamnan Jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya bayyana haka a wani jawabin faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen yaɗa labarai.

Ya kuma ce, INEC ba ta turo wakilanta ba domin sanya ido akan taron jam’iyyar, wanda ake gudanarwa a filin wasa na Lekan da ke Birnin Ibadan a Jihar Oyo.

Haka kuma gwamnan ya nesanta kansa da batun nan na sallamar Ministan Abuja, Nyesom Wike da wasu jiga-jigan jam’iyyar daga cikinta.

Haka ma takwaransa kuma Gwamnan Jihar Filato, Caleb Manasseh Mutfwang a wata sanarwa daga Kakakinsa, Gyang Bere, wanda ya ce ƙungiyar gwamnoni ba ta taɓa tattauna batun korar mambobin nata ba, sannan a kwamitin zartarwar jam’iyyar gabanin gabatar da shi a taron.

Ya bayyana cewa, babu hikima cikin korar wasu jiga-jigan jam’iyyar a yanzu musamman ganin yadda take buƙatar tattaro kawunan ƴaƴanta wajen dawo da martabarta.

By Babaji