Matsalar Tsaro: Kalubalen malamai da fastoci

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na ƙasar Faransa (AFP) ya fitar ya bayyana yunƙurin da wasu shugabannin addini daga ɓangaren Musulmi da Kirista a Ƙaramar Hukumar Mangu da ke Jihar Filato, a shiyyar Arewa ta Tsakiya, suke yi don dawo da zaman lafiya da kyakkyawar zamantakewa a tsakanin al’umma a yankin. Sakamakon wani mummunan rikicin addini da ya auku a wannan ƙaramar hukumar a shekarar 2024, wacce mazauna cikinta ke da daɗaɗɗen tarihin zaman lafiya.

Mazauna yankin na ganin hanyar samar da ɗorewar zaman lafiya ta dogara ne ga yadda malaman addini suka ba da ƙarfi wajen ƙarfafa muhimmancin zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai, ta cikin wa’azozinsu, da nisantar kalaman tunzura juna ko ɓatanci ga wani addini. Sannan harwayau, sun ƙudiri aniyar ganin sun gyara wuraren ibada, masallatai da coci-coci, da aka ƙona a lokacin rikicin. Wannan wata muhimmiyar dama ce ta sake ɗinke ɓarakar da ke tsakanin al’umma da rashin jituwa ta raba kansu.

A yayin da wannan rahoto ke fitowa, yana ƙara nuna jajircewar ‘yan Nijeriya, wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa a tsakanin su, duk kuwa da zargin da shugaban ƙasar Amurka Donald Trump, ya yi kan cewa, musulmi ’yan ta’adda masu tsattsauran ra’ayi suna yi wa Kirista, marasa rinjaye a Arewa, kisan kiyashi. A dalilin haka ne ma har yake barazanar kai harin soja kan maɓoyar waɗannan ƙungiyoyi. Barazanar da Gwamnatin Nijeriya ta yi watsi da ita, tare da samun goyon bayan wasu ƙasashen duniya irin su Rasha da China.

Wasu rahotanni daga Amurka na bayyana cewa, babu makawa batun kawo wannan hari ya wuce barazana, domin kuwa hukumomin tsaron ƙasar sun kammala fitar da jadawalin yadda za su aiwatar da wannan ƙudiri nasu na fatattakar ’yan ta’adda a sassan arewacin Nijeriya. Duk kuwa da ƙoƙarin da jami’an diflomasiyya a Nijeriya ke yi na ganin an samu fahimtar juna tsakanin ƙasashen biyu. Amma wani abu da ya fi ɗaukar hankali shi ne yadda malaman addini na Kirista da Musulmi ke fitar da maganganu a wuraren wa’azozinsu da kafafen sada zumunta, irin maganganun da suke da tsoratarwa, da ƙara raba kan mutane.

Idan mutum ya bibiyi irin maganganun da ake yaɗawa da sharhin da mabiya suke yi, zai zaci ƙasar nan ta kusa ɓarkewa da yaƙi ne, ko tana gab da fashewa. Saboda kalmomi irin na ƙyamar juna da ƙiyayya da matasa ke jifan juna da su. Sai dai abin da ya fi illa shi ne wanda malamai da fastoci suke yi, waɗanda su ne ya kamata a ce suna tsawatarwa da jan hankalin matasa, a matsayinsu na masu aiki da hankali da ilimi.

Wani mai kiran kansa da Eɓangelist, wato mai wa’azin Kirista, ya yi wani rubutu a kafar sadarwa ta fesbuk, inda yake nuna cewa, jami’o’in Arewa ba sa ɗaukar ɗalibai Kirista ko waɗanda suka fito daga jihohin Kudu, domin su yi karatu a cikinsu. Haka kuma ba a ɗaukar wanda ba Musulmi ba aiki a jihohin Arewa. Irin waɗannan maganganu na shaci-faɗi za ka riƙa ji ko karantawa a shafukan sada zumunta, na rubutu ko na bidiyo, wasu saƙonnin ma ba daga waɗanda ke zaune a Arewa ba ne. Wasu ne kawai ’yan taya ɓera ɓari suke yaɗa ƙarairayi don kawai su sanya tsoro ko firgici a zukatan jama’a, waɗanɗa ka iya hasala yanayin da ake ciki.

Akwai wani babban mai wa’azin Kirista a Jihar Filato, dake da magoya baya da yawa da na ga ya rubuta wasu maganganu a game da halin da Kirista ke ciki, a jihohin tsakiyar Nijeriya, inda yake cewa a kullum a cikin ƙarar harbe-harben bindigogi suke kwana, sannan su wuni suna ƙirga gawarwaki da zuwa makabarta. Duk wanda ba a Arewa yake ba, ko bai zauna a manyan garuruwan tsakiyar Nijeriya ba, dole hankalinsa ya tashi daga jin irin waɗannan kalamai. Ballantana wanda yake da ’yan uwa da ke zaune a yankin, dole ya shiga damuwa.

A yayin da malamai daga ɓangaren Musulmi suke ƙoƙarin ƙaryata zargin babu wani kisan kiyashi da ke faruwa ko kuma tabbatar da cewa kashe-kashen da ake yi yana shafar kowanne ɓangare, amma za ka ji ana amfani da kalmomin dake nuna dama abokan zaman mu ba ƙaunar mu suke yi ba, dole musan shirin da za mu yi don mu kare kan mu daga abin da zai iya biyowa baya da sauransu. Haka a ɓangaren Kirista, akasari fastocin da ke yaɗa maganganu na tunzura jama’a ƙoƙarin da suke yi shi ne fitar da wasu bayanai da adadin waɗanda aka kashe a hare-haren da ake kaiwa a ƙauyuka, da waɗanda rikicin ƙabilanci yake rutsawa da su. Da dama daga cikin alƙaluman da ake fitarwa aringizo ne ko ba gaskiya ba ne.

A ganina, babu abin da ƙasar nan ke buƙata a halin yanzu irin addu’a da kuma ƙoƙarin fahimtar da ’yan ƙasa muhimmancin haɗin kai, da nisantar kalaman tunzura juna, ko yaɗa labaran ƙarya. Fatan mu shi ne, jami’an tsaron Amurka ba za su zo su haddasa mana yaƙin basasar addini ba, ko su yi ta jefa bamabamai kan fararen hula da wuraren zaman jama’a ba. Ko su haddasa mana wani tawaye na kifar da zaɓaɓɓiyar gwamnati, don su ɗora karnukan farautar su, waɗanda za su riƙa sace mana arzikin ƙasa suna kaiwa Amurka ba.

Burin mu shi ne, idan har zuwan su ƙasar nan ya zama lallai babu makawa to, su yi aiki tare da jajirtattun sojojin ƙasar nan, domin gano maɓoyar ɓatagari da daƙile duk wani mugun nufi nufinsu akan talakawan ƙasar nan da ba su ji ba, ba su gani ba. Kuma kada aikin da za su yi ya shafi tsarin zamantakewar mu, na al’ada, harkokinmu na addini, masarautunmu na gargajiya, da dimukraɗiyyar mu. Sannan kada su haɗa kai da wasun mu da za su riƙa satar musu bayanai, suna taya su leƙen asiri a cikin ƙasar mu, da nufin haddasa mana rashin yarda da juna da fitintinu da  za su angiza mu faɗa da juna. Domin ba tun yanzu ba mun san Amurka, kanwa ce uwar gami. Kuma jaɓa ce, duk inda ta tsoma baki sai ta gurɓata.

Sai dai wani abin tsoratarwa a wannan dambarwa shi ne yadda wasu rahotanni daga Amurka suka bayyana cewa, Majalisar Dokokin ƙasar ta sanar da shirin sanya takunkumi da riƙe kadarorin wasu shugabannin ƙungiyoyin Fulani na Miyetti Allah da Miyetti Allah Kautal Hore dake Amurka, saboda zargin su da taimakawa ayyukan ta’addanci. Wannan na nuna cewa, Amurka ta ɗauki ɓangare a wannan dambarwa, ba ƙoƙarin sasantawa da samar da zaman lafiya take yi ba. Domin hakan na nuna, Amurka ta ɗora alhakin zaman doya da manja da ake samu tsakanin makiyaya da manoma a yankin tsakiyar Nijeriya, da rikicin ƙabilanci dake faruwa, akan al’ummar Fulani bakiɗaya, ba wai ’yan ta’adda ba. Hakan kuwa babban kuskure ne! Kodayake, tuni ƙungiyoyin sun ƙaryata zarge-zargen da ake yi wa mambobinta da kuma nuna rashin jin daɗinsu na yadda aka danganta su da ’yan ta’addan da suke yaƙi da su.

Dole ne ’yan Arewa su nuna fargaba da tsoro kan shigowar Amurka cikin matsalolin tsaron Nijeriya, domin sanin cewa ba za a yi musu adalci ba. Yadda ake kallon dukkan Fulani a matsayin ’yan ta’adda, haka za a zo matakin da za a ɗauki shugabannin Musulmi na addini da na siyasa, a matsayin masu ɗaukar nauyin ta’addanci, ko goyon bayan ’yan ta’adda. Babu wani mutum daga Arewa, da zai fito ya nuna an yi ba daidai ba, ko kuma a gyara kaza, sai an yi masa kallon mai goyon bayan ta’addanci.

Muna fatan ubangiji Allah Ya kawo mana zaman lafiya da ingataccen tsaro a Arewa da Nijeriya bakiɗaya.

By ukarofi