Daga AISHA ASAS
Cin zarafin mata a masana’antun fina-finai wani labari ne da ba ya tsufa, kuma yake yawan taka rawa lokaci zuwa lokaci, wanda a duk lokacin da ya taso yakan yi amon da za a ajiye komai a ba shi masauki na ɗan lokaci kafin a koma kan wasu ababen na daban.
Kuma abinda ke ɗaure kai shi ne, a duk lokacin da ya taso a wata masana’anta sautinsa kan kai ga takwaranta ta wani ɓangare na duniya har ido ya kai can wanda zai yi wuya ba a samu wani koke a ɓangaren ba.
Da wannan wasu ke ganin zargi ne da ba shi da tushe, wanda suka ɗora alhakin hakan a neman shuhura da matan ke yi wanda suke amfani da hanyar tausayi don samun biyan buƙata. Saidai tambayar da na kasa samun amsar ta, shin ya aka yi wannan ɗabi’a ta “zargi da ba shi da tushe” ta samu karɓuwa a dukan masana’antun fim da suke kewaye a duniya?
A wani ɓangare kuwa martanin mutane kan cin zarafin mata a harkar fim na kasancewa “ruwan dare” wanda suke cewa ya zama al’adar harkar fim, don haka suke ganin duk wadda ta kai kanta ta san abinda ke gudana, saboda haka bai kamata ta dinga yekuwar abinda ta riga ta san da shi tun kafin ta shigo. Kamar yadda wani Bature ya taɓa faɗa a wani lamari na wata jaruma da ta bayyana irin cin zarafin da aka yi mata, ya ce “Idan kin san ba za ki jure zafin ba, ki yi gaggawar barin kicin ɗin.”
Wannan na nufin a wata siga wasu suna kallon cin zafari musamman ga mata a masana’antun fim wata al’ada ce da duniyar ta nishaɗi ta gama ba wa masauki a cikinta.
Masana’antar fina-finai wata babbar cibiya ce da ke jagorantar harkar nishaɗantarwa, wadda ke bayar da dama masu yawa musamman ga mata, kuma hanya ce mai matuƙar tasiri ga cigaban tattalin arzikin ƙasa, wadda ke samar da ɗimbin ayyyuka ga mutane musamman ma matasa.
Jarumai a fina-finai sun zama taurari da mutane ke yawan nuna wa soyayya waɗanda a ƙasashe irin Najeriya ‘yan siyasa ke amfani da su wurin ranto masu soyayyar masoyansu. Wannan na ɗaya daga cikin dalilan da suka sa jama’a ke tururuwar zuwa ga masu harkan da fatan samun damar shiga layin waɗanda duniya za ta sani wanda hakan dama ce ba ƙarama.
Idan mun ɗauki ƙasashe irin Turai, za mu fahimci harkar fim a matsayin babbar sana’a da ke ba wa mai ita tarin arziki. inda jarumi zai iya mallakar abinda ɗan siyasa ma ba shi da shi sakamakon irin tsari da tasirin fina-finan nasu.
Wannan wata hanya ce da ke ƙara wa jaruman ƙima a idon duniya wanda ke sa a gan su a matsayin ‘untouchable’ ma’ana waɗanda ba su taɓuwa.
Dalilin kenan da ke sa mutane mamaki yayin da fitaciyyar jaruma ta fito ta koka kan cin zarafi, har ake ganin idan ma akwai wanda ya kamata ya ci zarafin ita ce saboda sunan da take da shi suke ganin ta fi ƙarfin hakan.
Shafin Taurari na wannan mako zai yi duba kan gaskiya ko rashin tasirin wannan zargi, inda za mu kawo wa masu karatu batutuwa daga masana da masu ruwa da tsaki kan harkar fim tun daga masan’antar fina-finai ta Amurak, wato Hollywood, Bollywood ta Indiya, Kannywood ta Arewacin Najeriya, da kuma takwaranta ta Kudu, Nollywood, don fahimtar gaskiyar lamarin, da inda matsalar take, ko dalilin samuwar ta ko rashin ta.
Bari mu fara daga tushe, wato Hollywood wadda ita ce uwa abin koyi ga masana’antun fim na duniya.
Kamar yadda alƙaluma suka bayyana, masana’antar Hollywood ita ce masana’antar fina-finai da ta fi kowacce masana’anta samar da kuɗin shiga tare da tsari ga jarumanta da ke sa su ci moriyar aikinsu ko bayan sun bar fitowa a fim.
An tabbatar da cewa, jaruman Hollywood na da kaso a duk wata riba da fim ɗin da suka yi ya samu. Yadda abin yake shi ne, za a biya jarumi kuɗin aikinsa na yin fim, sannan idan fim ɗin ya samu karɓuwa, ba kuma dole sai ya samu gagarumar karɓuwa ba, koda ba da yawa sosai ba, to a cikin ribar da aka samu, akwai wani abu da za a ba shi. Kuma haka za a dinga ba shi ita a duk lokacin da aka siyar da fim ɗin, ma’ana ba zai daina samun kaso daga fim ɗin ba har sai an daina siyan sa. Abinda za a ba shi kuwa ya danganta da irin yarjejeniyarsa da kamfanin da ya yi wa aiki.
Wannan na daga dalilan da ke sa kaga jarumin da bai yi fina-finan da suka kai 6 ba, amma yana da tarin dukiya, saboda wataƙila ya samu sa’ar duka sun karɓu, don haka an ci kasuwarsu sosai, kuma tare da shi ake cin romon su.
Wannan ne ya sa cikin ƙanƙanin lokaci jaruman Hollywood ke samun matsayi sosai, suna gina gidaje na alfarma, su hau motoci na zamani.
Duk wannan matsayi da cigaban da ke cikin wannan masana’anta, bai hana zargin cin zafarin mata hudowa a tsakanin ta ba. Domin rahotanni da dama sun bayyana matsalar cin zarafin mata a masana’antar a matsayin ruwan dare, inda alƙaluma suka nuna kaso 94 bisa 100 na matan masana’antar sun fuskanci wani daga cikin nau’ukun cin zarafi.
Wani sabon bincike na kwanan nan ya bayyana cewa, kashi 59 bisa 100 na mata a Hollywood sun aminta da cin zarafin mata a a masana’antar wata al’ada ce da ke da gurbin zama na dindindim.
Babban abin takaicin kuwa shi ne, wannan al’ada ta samu ɗaurin gindi ne kasancewar mazan da ke cin zarafin matan sun kasance masu manyan muƙamai ne ko in ce masu faɗa a ji a harkar, kamar darakta ko furodusa ko kuma masu ɗaukar nauyi. Wannan ne ya sa masu laifin ke sha, kuma dalilin da ke tirsasa wa matan rufe bakinsu, kasancewar nuna masu da ake yi ba wata mafita matuƙar suna son cika burin su na zama jarumai, sai sun rufe idonsu su daga kallon yadda aka mayar da su bayin da ba su da iko kan jikinsu.
Idan ba za mu iya tunawa, a can baya an taɓa samun labarin da ya tada ƙura, ba wai a Hollywood ba, a duniya baki ɗaya. Lamarin wanda ya shafi Harvey Weinstein ya janyo cece-kuce kan lamarin tasirin cin zafari a masana’antar, inda ya kasance babban mai faɗa a ji na kusan farko da aka zarga da cin zarafin mata, zargin da ya samu goyon baya da hujojji masu yawa.
Harvey Weinstein babban ɗan kasuwa ne a Hollywood wanda shi ne ya kafa Miramaɗ da The Weinstein Company tare da ɗan uwansa Bob Weinstein. Ya taka muhimmiyar rawa wajen shirya fina-finai da dama da suka yi fice kamar; ‘Shakespeare in Love’, ‘Pulp Fiction’, ‘The King’s Speech’, da sauransu. A taƙaice dai wani ginshiƙi ne da ya taimaki tubalin masana’antar tsayuwa da ƙafafunshi.
Daga shekarar 2017 jaridun The New York Times da kuma The New Yorker sun fitar da rahotanni masu tarin yawa inda suke zarrgin sa da cin zarafin mata da fyaɗe wanda rahotannin suka tabbatar da yana aikata wa tsayin shekaru 30.
ɗaya daga cikin tasirin wannan zargin akwai tayar da ƙungiyar MeToo Movement, ƙungiyar da ta ƙarfafa mata da maza kan bayyana yadda ake cin zarafinsu ta jima’a a wuraren aikinsu da ma wasu wuraren na daban.
Idan mun bi wannan lamarin har ƙarshe za mu fahimci cewa, ya tashi daga zargi, domin yanzu haka Weinstein yana gidan yari, bayan kotu ta same shi da laifin cin zarafin mata.
Wasu daga cikin matan da suka fito, suka faɗi cewa Weinstein ya ci zafarinsu akwai; Ashley Judd, ta bayyana cewa, Weinstein ya gayyace ta zuwa wani ɗaki a otel don tattauna wani fim, saidai take ya fara yunƙurin bayyana manufarsa.
“Na gane nan da nan cewa ba maganar aiki ba ce, saidai yunƙurin yin lalata da ni,” inji ta.
Sai kuma Rose McGowan, jaruma ce da ta jima tana ƙoƙarin bayyana koken ta. A cewar ta, Weinstein ya yi mata fyaɗe a shekarar 1997, ta kuma zargi Hollywood da ba shi kariya saboda gudun rasa ayyukan da yake jagoranta. A cewar ta, “Ba wai kawai mutum ɗaya ne ya zalince ni ba, tsarin masana’antar ce gaba ɗaya ta kare shi.”
Ita kuma jaruma Gwyneth Paltrow, ta bayyana cewa, yayin da take da shekaru 22, Weinstein ya taɓa nuna mata ra’ayin yin lalata da ita a lokacin da suka fara aiki tare. Sai ta sanar da saurayinta na lokacin Brad Pitt, wanda ya fusata sosai har ya tunkari Weistein.
“Na ji tsoro matuƙa, saboda makomata a fim a hannunsa take,” inji jaruma Gwyneth.
Hakama fitacciyar jaruma Angelina Jolie ta bayana ta ƙi yin aiki da Weintstein gaba ɗaya bayan wani yunƙuri da ya yi mata na lalata a farkon aikinta. A cewar ta “Na ji abin sosai kuma ya yi muni, don haka daga baya na ƙi ko tuntuɓar kamfaninsa.”
Waɗannan na daga cikin dubatan matan da suka cire tsoro suka bayyana irin cin zarafin da wannan mutumin ya yi masu, yayin da ta sandiyyar wannan lamari ne aka dinga samun wasu suna bayyana wani ɓangaren da cin zarafin ya samu matsugunni wanda a baya ba a san da shi ba. Kuma ba wai a iya mata cin zarafin ya tsaya ba, domin wasu rahotanni sun bayyana mazan ma ba a bar su ba, hakan na da alaƙa ne da irin wurin da shi namijin ya samu kansa. Saidai an tabbatar da na matan dai ya fi yawaita.
Da wannan za mu iya cewa, a Hollywood cin zarafi bai zama ɓata suna kawai ba, domin ko akwai waɗanda aka yi wa ƙazafi, akwai waɗanda tabbas sun aikata tunda har shari’a ta kai ga hutunta su.
To shin ko haka take a Masana’antar Bollywood ta Indiya?
Za mu ci gaba mako mai zuwa.
