
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce ta warware Naira biliyan 4.2 domin amfani da su wajen daƙile aukuwar ambaliyar ruwan sama da ayyukan bada agajin gaggawa ga iftila’in.
Shugaban kwamitocin kula da lamuran agajin gaggawa a jihar, Dakta Abdullahi Sa’id ya faɗi hakan a yayin zama da masu-ruwa-da-tsaki game da lamarin a ranar Laraba, a garin Ringim dake Ƙaramar Hukumar Ringim a jihar.
An gudanar da zaman ne a ƙarƙashin Hukumomin kula da muhalli da Bada Agajin Gaggawa na jihar duba da cewa jihar tana ɗaya daga cikin jihohin da ka iya fuskantar ambaliya, kamar yadda Hukumar Kula da Yanayi (NiMET) ta yi hasashe.
Dakta Sa’id ya ce, an ware kuɗaɗen ne da nufin samar da hanyoyin rage barazanar ambaliya da bunƙasa ayyukan hukumomin bada agajin gaggawa a ƙananan hukumomi 27 dake faɗin jihar.
Ya kuma ce, gwamnatin jihar ta naɗa mataimakan ciyamomin ƙananan hukumomin domin su jagorancin tawagogin ayyukan ƙaurace wa ambaliya da sauran ayyukan da suka shafe ta ta yadda ya dace.
Kazalika, akan hasashen NiMET ne kowace ƙaramar hukuma a jihar ta tara Naira miliyan 11 domin riga-kafin ambaliya a garuruwa da ƙauyukansu.
