Amurka ta aikata assha da sunan asusun NED

Daga CMG HAUSA

Ƙila wasu sun san asusun demokuraɗiyya na ƙasar Amurka, saboda sunan asusun ya ambato demokuraɗiyya wato NED. Amma mene ne gaskiyar asusun? Kwanan baya, ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin ta fitar da wasu jerin shaidu a shafinta na Internet, inda ta bankaɗo asirin asusun. Haƙiƙa asusun NED ya ƙulla maƙarƙashiya da yawa a sassan duniya, kamar ta da rikicin kawo ɓaraka, yin juya juyin mulki, rikicin siyasa, yin ƙarya da yaɗa jita-jita da dai sauransu. Ba za a iya lissafa laifuffukan da asusun na NED ya aikata ba. Ƙila ayyukan assha da ya aikata za su wuce zaton mutane.

An kafa asusun NED a matsayin ƙungiya mai zaman kanta a shekarar 1983, da sunan bai wa ƙasashen duniya tallafin demokuraɗiyya, amma a haƙiƙa yana gudanar da aikace-aikacen na keta tsarin demokuraɗiyya.

Ƙasar Sin tana ɗaya daga cikin wuraren da asusun NED ya faɗaɗa aikin makircinsa. Inda ya rura wutar fitina dangane da batutuwan Hong Kong, Taiwan, Xinjiang da Tibet.

Dimbin shaidu na zahiri sun nuna cewa, Amurka ta fake da asusun NED, tana tsoma baki a harkokin cikin gida na wasu ƙasashe, a ƙoƙarin samun moriya. Asusun ba ya ƙoƙarin shimfida demokuraɗiyya, illa yunƙurin hamɓarar da gwamnatin wasu ƙasashe da kawo musu ɓaraka, ta yadda Amurka za ta samu riba, har ma ta ci gaba da yin danniya a duniya.

Fassarawa: Tasallah Yuan