Amurka ba ta da izinin zargin jama’ar Afirka kan zaɓin yin haɗin gwiwa tare da Sin

Daga CMG HAUSA

A yayin ziyarar da mataimakiyar sakataren harkokin wajen ƙasar Amurka Wendy Sherman ta yi a nahiyar Afirka, ta bayyana cewa, wasu ƙasashen Afirka sun zabi kamfanin Huawei na ƙasar Sin a matsayin kamfanin dake samar da hidimar sadarwa, wai wadannan ƙasashe sun yi watsi da ikon mulkin kasa. Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, zargin da jami’ar Amurka ta yi kan ƙasar Sin ba shi da tushe. Ya rage ga ƙasashen Afirka da jama’ar su zabi waɗanda za su yi hadin gwiwa da su, kuma ba Amurka ba ce ta yanke hukunci.

Zhao Lijian ya bayyana cewa, ra’ayin madam Sherman ta shaida yunkurinta na kin ƙasar Sin da tada rikici a tsakanin Sin da Afirka. Kamfanonin Sin ciki har da kamfanin Huawei suna gudanar da hadin gwiwa mai kyau tare da ƙasashen Afirka da ma sauran ƙasashen duniya da dama, wanda ta sa ƙaimi ga kyautata da bunƙasa ababen more rayuwar jama’a ta aikin sadarwa, da samar wa mazauna wurin hidimar sadarwa ta zamani mai inganci da tsaro da kuma araha, wanda ta samu karɓuwa sosai a wajen jama’a. A yayin da ake yin haɗin gwiwar, ba a samu wata matsala ta batun leƙen asiri ko kawo illa ga tsaron yanar gizo ko ɗaya ba.

Mai Fassara: Zainab