Ƙasashen Afirka sun yi shiru don nuna ƙin amincewa ga ƙasashen Yamma

Daga CMG HAUSA

Bayan ɓarkewar yaki tsakanin Rasha da Ukraine, Amurka da wasu ƙasashen yamma na ƙoƙarin mai da ƙasar Rasha saniyar ware, inda suke matsawa sauran ƙasashe lamba, domin su goyi bayansu. Hakan ya sa wasu jami’an ƙasar Amurka ke daga murya ga ƙasashen Afirka, don su yi watsi da matsayinsu na ‘yan ba ruwanmu. Duk da haka, yayin da ake jefa kuri’a a Majalisar Ɗinkin Duniya don tabbatar da cewa ko za a yi Allah wadai da ƙasar Rasha, akwai ƙasashe 25 dake nahiyar Afirka da suka jefa ƙuri’ar janyewa daga batun, ko kuma kin jefa ƙuri’ar.

To, me ya sa waɗannan ƙasashen Afirka suka yi shiru duk da matsin lambar da su ƙasashen yamma suke yi?

Saboda da farko dai, ko da yake rikicin Rasha da Ukraine na nisa da nahiyar Afirka, amma yana jefa al’ummar Afirka cikin wahala sosai.

Yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine ya sa ƙasashen Afirka fuskantar matsalar ƙaranci, da hauhawar farashin abinci, inda farashin alkama ya riga ya ƙaru da kashi 60%. Baya ga yadda yaƙi yake tsananta matsalolin da Afirka ke fuskantar, a fannonin makamashi, da hada-hadar kuɗi. Amurka da sauran ƙasashen Turai na kokarin tura makamai ga ƙasar Ukraine, don neman raunata ƙasar Rasha bisa ɗorewar yake-yake. Sai dai hakan ba zai amfani ƙasashen Afirka ba, domin dorewar yakin ita ma za ta cusa ƙasashen Afirka cikin wahala matuka.

Ban da haka kuma, yadda su ƙasashen Afirka suka ki goyon bayan ƙasashen yamma, shi ma ya shafi wasu ayyukan da ƙungiyar tsaro ta NATO ta yi a baya.

Jama’ar ƙasashen Afirka ba za su manta da shishigin da sojojin ƙasashen NATO suka yi a ƙasar Libya ba, lamarin da ya sa ƙasar ta tsunduma cikin yanayi na rikici. Kana wannan yanayi ya haifar da ta’addanci. Bayan da aka hamɓarar da gwamnatin Ghaddafi, ƙasar Libya na ta fama da matsalar hare-haren ‘yan ta’adda, kana wannan matsala na yaduwa zuwa ƙasashe maƙwabtan ƙasar cikin sauri.

Zuwa yanzu, jama’ar ƙasashen Najeriya, da Nijar, da Mali, da sauransu, suna shan wahalar hare-haren ta’addanci da ‘yan fashi, kuma asalin waɗannan matsaloli shi ne yaki “na adalci” da ƙungiyar NATO ta ƙaddamar a ƙasar Libya a shekarar 2011. Haƙiƙa ƙungiyar NATO ita ma tana da hannu cikin yaƙin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine. Shugaban ƙasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya taba bayyana cewa, akwai damar magance yaƙi, idan har kungiyar NATO ta yi haƙuri da kwaɗayinta na faɗaɗa zuwa yankunan gabashin duniya.

Sa’an nan yadda ƙasashen Afirka suka juya baya ga ƙasashen yamma a wannan karo, shi ma ya nuna takaicinsu kan bambancin da ƙasashen yamma suka nuna musu.

Bayan ɓarkewar yaƙi a Ukraine, yayin da al’ummomin ƙasashen Afirka da suke zama a ƙasar suka yi ƙoƙarin ficewa, akwai wasu ‘yan ƙasar Ukraine da Poland da suka nuna musu kyama da wulaƙanci a lokacin. Ko da yake ƙasar Amurka tana neman dukkan ƙasashen duniya su yi Allah wadai da ƙasar Rasha, amma ta yi shiru game da abubuwan da Ukraine da Poland suka yi na nuna bambancin launin fata.

A nata ɓangaren, gwamnatin ƙasar Birtaniya ta yi alƙawarin karɓar ‘yan gudun hijira dubu 200 daga ƙasar Ukraine, yayin da a lokaci daya kuma take neman tusa keyar ‘yan gudun hijira daga nahiyar Afirka, don su koma ƙasar Rwanda dake nahiyar Afirka.

Ganin yadda ƙasashen yammacin duniya suke ƙoƙarin ɗaukar manufofi na son kai, ya sa ƙasashen Afirka yin shiru game da bukatunsu. Hakan ya nuna ra’ayin ƙasashen Afirka, wato ba za su ci gaba da biyayya ga maslahar ƙasashen yamma ba, inda za su dauki manufar da za ta tabbatar da moriyarsu, bisa son ransu.

Mai Fassara: Bello Wang