APC za ta samar da daidaito ga duk masu son tsayawa takara – Adamu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, ya tabbatar wa duk masu neman muƙamai daban-daban a faɗin ƙasar nan cewa, jam’iyyar za ta yi gaskiya da samar da daidaito a lokacin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar mai zuwa.

Adamu ya bayar da wannan tabbacin ne a ƙaramar hukumar Keffi ta jihar Nasarawa a ranar Lahadin da ta gabata a lokacin da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a shiyyar sanata ta Yamma suka gudanar da wani taro na nuna ɓangaranci da karrama shi.

Ya kuma yaba wa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar bisa wannan karramawar da aka yi masa, ya kuma yi kira da a yi masa addu’a da goyon baya domin ya samu nasarar gudanar da aikin da ke gabansa.

Adamu wanda ya yi magana ta bakin kakakin majalisar dokokin jihar Ibrahim Abdullahi, ya jaddada buƙatar jam’iyyar ta cigaba da kasancewa a dunƙule wuri guda, ya kuma buƙaci masu sha’awar tsayawa takara da su amince da sakamakon zaɓen fidda gwanin da za a yi cikin gaskiya da riƙon amana da kuma ƙolarin ganin jam’iyyar ta samu nasara a lokacin babban zaɓen 2023.

Ya ce, “ina so na tabbatar wa kowa da kowa cewa jam’iyyar za ta samar da daidaito ga duk masu neman muƙamai daban-daban a lokacin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC mai zuwa”.