Dalilan ASUU na sake tsawaita wa’adin yajin aikinta da watanni uku

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta bayyana cewa, ta tsawaita wa’adin yajin aikin da take tsaka da gudanar da makonni 12 saboda rashin yin abin da ya kamata daga ɓangaren Gwamnatin Tarayya.

Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana tsawaita wa’adin yajin aikin a ranar Litinin, yana mai cewa sun ɗauki wannan mataki ne domin bai wa Gwamnati isasshen lokaci wajen warware matsalolin da suka gabatar mata.

Ya ƙara da cewa, tsawaita wa’adin yajin aikin ya fara aiki ne daga kan ƙarfe 12:01am na ranar 9 ga Mayun 2022.

Haka nan, ya ce sun yanke shawarar tsawaita wa’adin ne bayan taron Majalisar Zartarwa na Ƙasa na ASUU wanda suka soma cikin daren Lahadi a Jami’ar Abuja.

“Bayan zazzafar tattauna tare da la’akari da gazawar Gwamnatin wajen yin abin da ya kamata na warware matsalolin da aka gabatar a yarjejeniyar da aka cin ma tsakaninta da ASUU a 2020 a cikin wa’adin da aka ɗibar mata tun farko, majalisar shugabannin ASUU ta yanke shawarar sake tsawaita wa’adin yajin aikin da ASUU ke kan yi da makonni 12 don bai wa gwamnati isasshen lokaci wajen magance buƙatun ASUU da ke gabanta,” inji sanarwar.