Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ofishin jakadancin Amurka da ke Nijeriya ya fitar da sanarwar tsaro inda ya gargaɗi ‘yan kasarsa kan yiwuwar harin ta’addanci da ka iya shafar cibiyoyinta da kuma makarantu masu alaka da ƙasar a fadin Nijeriya.
A sanarwar da ofishin jakadancin da ke Abuja ya fitar, an buƙaci ‘yan Amurka su ƙara yin taka-tsantsan idan za su ziyarci ofisoshin diflomasiyyar Amurka ko kuma cibiyoyin da ke da alaƙa da ƙasar.
Sanarwar ta ambaci ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja da kuma ƙaramin ofishin jakadancinta da ke Legas, inda aka buƙaci ‘yan ƙasar su kasance cikin lura tare da ɗaukar ƙarin matakan tsaro idan za su je waɗannan wurare.
Ofishin jakadancin ya ce “yana da muhimmanci mutane su riƙa canza hanyoyin tafiya da lokutan da suke fita, su guji yin abu iri ɗaya a kai a kai, tare da kasancewa masu lura da abubuwan da ke faruwa a muhallinsu domin rage haɗarin da ka iya tasowa.”
Sanarwar ta ce: “Ya kamata ‘yan Amurka su ɗauki ƙarin matakan tsaro idan suna tafiya zuwa ofishin jakadancin ƙasar da ke Abuja, ko ƙaramin ofishin jakadancin ƙasar da ke Legas, da kuma makarantu masu alaƙa da Amurka.”
Haka kuma sanarwar ta shawarci ‘yan ƙasar da su guji cunkoson jama’a ko zanga-zanga, sannan su sake duba tsare-tsaren tsaron kansu tare da iyalansu.
Sauran matakan kariya da ofishin ya bayar sun haɗa da tabbatar da cewa wayoyin hannu suna da caji idan wani lamarin gaggawa ta taso, da kuma sanin hanyoyin fita na gaggawa idan aka shiga wani gini.
