Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rikici tsakanin ’yan ƙabilun Tibi da Jukun a garin Fatakwal da ke Jihar Ribas ya haddasa tashin hankali, inda aka kai hari kan wasu ’yan Arewa har da ƙona masallaci.
Wakilin Manhaja ya samu labarin cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin, bayan wani ɗan ƙabilar Jukun ya kashe wani ɗan ƙabilar Tibi a wata rigima da ta ɓarke a kasuwar Eneme Junction da ke Fatakwal.
Wata majiya da ta shaida faruwar lamarin ta bayyana cewa duka mutanen biyu ’yan asalin Jihar Taraba ne, kuma mabiya addinin Kirista ne.
Ya ce rikicin ya samo asali ne lokacin da ɗan ƙabilar Tibi ya kasa kayansa domin sayarwa a kasuwar, sai wani ɗan kabilar Jukun ya zo ya ajiye baronsa kusa da wurin.
A cewar majiyar, ɗan kabilar Tibi ya nemi Bajukunin da ya matsa daga wurin, amma ya ƙi tashi.
Daga nan ne saɓani ya rikiɗe zuwa tashin hankali tsakanin su, inda ake zargin ɗan kabilar Jukun ya daɓa wa ɗan ƙabilar Tibi wuƙa a ciki, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa nan take.
Majiyar ta ƙara da cewa bayan aukuwar kisan, wasu fusatattun matasa a yankin sun juya lamarin zuwa rikicin addini, duk da cewa dukkansu mabiya addinin Kirista ne.
An ce matasan sun kai hari kan wasu ’yan Arewa da ke zaune a yankin, inda suka raunata mutane da dama tare da ƙona masallaci.
Har ila yau, an ruwaito cewa an yi barazanar korar ’yan Arewa daga yankin, ba tare da la’akari da cewa rikicin na ƙabilanci ne ba na addini ba.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Sarkin Hausawan Fatakwal, Alhaji Hussain Madaki, ya ce rikicin ya samo asali ne daga saɓani tsakanin ɗan kabilar Tibi da na Jukun kan wurin sayar da kaya a kasuwa.
Ya jaddada cewa dukkansu Kiristoci ne, kuma bai kamata a mayar da lamarin na addini ba.
Sarkin ya ƙara da cewa an kai hari kan ’yan Arewa tare da ƙona masallaci, amma a halin yanzu an samu kwanciyar hankali bayan jami’an tsaro sun shiga tsakani.
