
Shirye-shirye sun kammala yayin da Shugaban Ƙasa ya sanar da sabon shugaban Hukumar Zaɓe, INEC bayan da Farfesa Mahmood Yakubu ya kammala wa’adin mulkinsa na shekara 10 a ranar Talata.
Kafin Yakubu ya sauka daga muƙamin, rahotanni sun nuna cewa Fadar Shugaban Ƙasa na nazarin mutum uku da ake hasashen za su iya maye gurbin nasa.
Mutanen sune Farfesa Joash Ojo Amupitan da Mai Shari’a Abdullahi Mohammed Liman da kuma Farfesa Lai Olurode.
Wata majiya daga Fadar Shugaban ƙasar ta shaida wa manema labarai cewa an kammala nazari, kuma Farfesa Amupitan ne ke kan gaba a jerin waɗanda ake hasashen maye gurbin tsohon shugaban na INEC.
Farfesa Yakubu ya sauka daga mukamin ne bayan ganawa da kwamishinonin zaɓe na jihohi a hedikwatar hukumar da ke Abuja.
A yayin haka ne ya miƙa ragamar shugabanci ga May Agbamuche-Mbu, wata kwamishiniya a hukumar, wadda ta karɓi mukamin a matsayin shugabar rikon ƙwarya.
