An gudanar da gasar harshen Sinanci ta Chinese Bridge ga ɗaliban jami’a da na sakandare a Uganda

Daga CMG HAUSA

An gudanar da gasar harshen Sinanci ta Chinese Bridge, ga daliban sakandare da jami’a, a cibiyar Confucius ta jami’ar Makerere dake Uganda.

Taken gasar na bana, na rukunin ɗaliban jami’a shi ne, “Duniya Guda, Iyali Guda” yayin da na daliban sakandare ya kasance “Kwarewa a Harshen Sinanci”.

Da yake jawabi a wajen gasar da aka yi ranar Asabar, jakadan Sin a Uganda Zhang Lizhong, ya ce gasar ta inganta musayar al’adu tsakanin ƙasashen biyu, kuma ta zama wani dandali da ɗalibai ke ƙulla abota.

Ita kuwa daraktar cibiyar tsara manhajar karatu ta ƙasar, Grace Baguma, cewa ta yi, ana samun karin malaman dake ɗaukar kwas-kwasan Sinanci, kuma a yanzu, ana koyar da harshen a matakin sakandare.

A cewar Gilbert Gumoshabe, daraktan cibiyar Confucius ta jami’ar Makerere, ta hanyar gasar Chinese Bridge, sun gane cewa dukkan mutane ɗaya ne, babu bambanci.

Fassarawar Fa’iza Mustapha