Ku gafarce ni, kuskuren da na aikata ba zai maimata kansa ba, Sufin Zamani ga MOPPAN

Daga BASHIR ISAH

Mawaƙin nan Sarfilu Umar da aka fi sani da Sufin Zamani, ya rubuta wasiƙa zuwa ga ƙungiyar masu shirya finafinai ta MOPPAN yana mai neman afuwa a kan ɓatancin da ya yi wa matan Kannywood cikin wata waƙarsa da ya yi.

Mawaƙin ya yi hakan ne don cika jerin sharuɗɗan da hukumar DSS ta gindaya masa bayan da hukumar ta same shi da aikata laifin da aka tuhume shi a kansa.

Bayan da MOPPAN ta samu ƙorafin matan Kannywood kan ɓantancin da mawaƙin ya yi musu ne, daga nan ta gurfanar da shi gaban DSS don bincike wanda a ƙarshe aka tabbatar da faruwar hakan.

Cikin wasiƙar da ya rubuta mai ɗauke da sa hannunsa, Sarfilu Umar ya ce: “Ina mai neman afuwar wannan ƙungiya ta MOPPAN mai albarka bisa kuskuren da na yi na yin waƙar da ta ɓata wa ‘yan masana’antar Kannywood rai.

“Allah ya sa ni ban yi wannan waƙa don na ɓata wa wani ko wata rai ba.

“Saboda haka ina neman afuwarku. Kuma Insha Allahu hakan ba za ta sake faruwa ba,” inji wasiƙar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *