Ƙasar Sin na adawa da duk wani yunquri na ɓata sunan shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya”

Daga CMG HAUSA

Game da sabuwar shawarar inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma, wadda ƙasashen G7 suka gabatar, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yau Litinin cewa, ƙasarsa har kullum tana maraba da duk wata shawarar dake inganta muhimman ababen more rayuwar al’ummar duniya, kana shawarwari daban-daban ba za su iya maye gurbin juna ba.

Ya ce ƙasar Sin na nuna adawa ga duk wani yunƙuri na bata sunan shawarar “ziri daya da hanya ɗaya”, bisa hujjar inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma, don cimma muradun siyasa.

Rahotanni sun ce, kwanan nan, a wajen taron ƙolin ƙasashen G7, shugaban ƙasar Amurka Joe Biden, ya sanar da ƙaddamar da “dangantakar abokantaka ta inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma da zuba jari a duniya”, kana wasu manyan jami’an gwamnatin Amurka da ba’a san ko su waye ba, sun rika furta kalamai na shafawa shawarar “ziri ɗaya da hanya daya” ta ƙasar Sin bakin fenti.

Rahotannin sun kuma ce, a ranar 25 ga wata, wani jami’in kwamitin tsaron ƙasa na fadar White House ta Amurka mai suna John Kirby, ya yi magana kan taron ƙolin ƙasashen G7, inda ya sake jaddada batun da ya shafi wai “yin aikin tilas” a ƙasar Sin.

Game da wannan batu, Zhao Lijian ya ce, yin aikin tilas, ba a ƙasar Sin yake faruwa ba, a Amurka yake wakana. Sai dai domin neman cimma muradunta na amfani da batun jihar Xinjiang, don kawo cikas ga ci gaban ƙasar Sin, Amurka ta sha kitsa ƙarairayi dake cewa wai, ana tilastawa al’umma aiki a Xinjiang. Amma haƙiƙanin gaskiya ita ce, irin zargin da Amurka ta yiwa ƙasar Sin, ya shaida laifin da ita kanta take aikatawa.

Fassarawar Murtala Zhang