Daga BASHIR ISAH
Alƙalin Alƙalan Nijeriya, Mai Shari’a Tanko Muhammad, ya yi murabus daga aiki.
Majiyar tashar Channels Television ta ce Jastis Muhammad ya yi murabus ne a Lahadin da ta gabata saboda dalili na rashin lafiya.
Bayanai sun nuna cewa, an yi nisa da shirye-shirye don rantsar da Alƙali mafi girman muƙami a Kotun Ƙoli, wato Jatis Olukayode Ariwoola, a matsayin Alƙalin Alƙalan Nijeriya mai riƙon ƙwarya.
Haka nan, bayanan sun ce nan ba daɗewa ba za a sanar da naɗin a hukumance.
Kafin yin murabus, rahotanni sun tabbatar da Jastis Muhammad na fama da rashin lafiya sosai.
Idan dai ba a manta ba, a makon da ya gabata ne alƙalan Kotun Ƙolin su 14, suka rubuta wa Muhammad takardar ƙorafi game da taɓarɓarewar yanayin aiki a kotun.
Inda a cikin wasiƙar, alƙalan suka zargi Muhammad da rashin magance matsalolin da suka dabaibaye musu yanyin aikinsu a kotun, da suka haɗa da rashin motocin aiki, rashin muhali, ƙarancin wutar lantarki da sauransu.