Kamfanin mai na Nijeriya ya samu lambar yabo kan ingancin kaya daga Turai

Daga AMINA YUSUF ALI

A kwanakin nan ne dai wani kamfanin mai na asalin Nijeriya mai suna MOAHZ Oil and Gas, Wanda ɗaya ne daga cikin kamfanonin da suke ƙarƙashin rukunin kamfanoni na MOAHZ group, ya samu nasarar amsar kambun yabo daga ƙasar Turai saboda ingancin kaya da harkokinsa.

Majalisar cinikayya ta ƙasar Birtaniya (EBA) ita ce ta jagoranci shirya taron da ba da wannan kambun girmamawar.

A yayin da yake jawabin taya murna, shugabar gudanarwa ta majalisar EBA, Malama Anna Jones, ta bayyana cewa, manufar wannan taron ba da kyaututtukan da karramawa mai taken, ‘Karramawar ingancin kaya na Duniya na Turai’ shi ne don ƙarfafa wa kamfanoni wajen cigaba da samar da ingantattun kaya da ayyuka.

A cewar Malaman Anna, waɗannan lambobin yabo da majalisar tasu ta raba, ta ba miƙa su ne ga kamfanonin da suka yi zarra a Duniya wajen samar da kayayyaki masu inganci da ayyuka.

Sannan a cewarta, an gudanar da zaɓen ne ta hanyar bincike a kan kamfanoni da dama da suke faɗin yankin Turai da ma na Duniya bakiɗaya.

A cewarta, a yayin zaɓen sun kula da abubuwa kamar haka a kowanne kamfani: nasarori, hanyoyin kiyaye haɗurran na kamfanin, tsaron muhalli, ingancin kaya, walwalar ma’aikatansa, da sauransu. Bayan tankaɗe da rairaya ne, sai kamfanin MOAHZ Oil and Gas, Afirka ya lashe gasar.

Daga ƙarshe ta yi amfani da damar don taya shugaban rukunin kamfanonin MOAHZ Oil and Gas, Dakta Abdulqadir Ojo murna a kan wannan lambar yabo da ya samu daga Turai wacce ya cancanci a ba shi ɗin. Sannan a cewar ta amsar lambar yabo daga Turai ba ƙaramar nasara ba ce da za ta iya jawo ɗaukaka mai girma ga kamfanin MOAHZ Oil and Gas.

A nasa jawabin, shugaban rukunin kamfanonin MOAHZ, Dakta Abdulqadir Ojo, ya bayyana cewa, wannan lambar yabo ta samu ne sakamakon shekaru masu yawa da kamfanin ya ɗauka yana gudanar aiki tuƙuru don samar da kaya da ayyuka masu inganci tare da mayar da hankali kacokan wajen sauraren abokan ciniki don gamsar da su.

Shi dai rukunin kamfanoni na MOAHZ group yana tafiyar da manyan kamfanni masu zaman kansu da suke ƙarƙashinsa kamar haka: MOAHZ Oil and Gas, MOAHZ Engineering & Project Management, MOAHZ investment, Green Mozaq Classic limited, da kuma MOAHZ Multi-Purpose Integrated services.

Kirifto Karansi da Hada-hadarsa dukka gaibu ne – Biloniya Bill Gates