Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Al’ummar ƙaramar Hukumar Gwoza da ke Jihar Borno sun koka kan yadda ’yan gudun hijira 91,007 suka warwatsu a sansanoni daban-daban a Nijeriya da Kamaru.
Mai magana da yawun ’yan gudun hijirar, Ayuba John Bassa, a wani taron manema labarai a Abuja ranar Juma’a ya ce, “’yan gudun hijira 50,000 na zaune tare da ‘yan uwansu a faɗin ƙasar nan.”
Ya ƙara da cewa, “rashin samar da musu da tsayayyen matsaguni ya zama nauyi akan wasu.”
Ya ce: “A yanzu an yi watsi da wasu ‘yan gudun hijira 550 a sansanin Kamaru; da yawa da suka yi ƙoƙari su koma Nijeriya da ƙafa sun mutu ko kuma sun sha wahala sosai a kan hanya.”
Bassa ya yi kira ga gwamnatin tarayya da dukkanin hukumomin da abin ya shafa da su ɗauki matakin ba tare da ɓata lokaci ba don dawo da martaba, adalci da tabbatar da ɗorewar mafita ga ‘yan gudun hijirar yankin.
Ya yi kira na musamman ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya maido da gidajensu da ’ya’yansu da martabarsu tare da sakin kayayyakin da aka yi kasafin kuɗin tafiyar da rayuwarsu.
Kakakin da ke garin Gwoza ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2013, an tilastawa mutane da dama daga yankin yin hijira tare da raba wasu daga gidajensu a faɗin Nijeriya da Kamaru sakamakon rikicin Boko Haram.
Ya koka da yadda adadin ‘yan gudun hijira ya kai 91,007, waɗanda suka warwatse a sansanoni daban-daban a Nijeriya da Kamaru.
A cewar Bassa, an sha samun tauye haƙƙin yara 17, inda ya ba da misali da batun wasu yara 17 da ake zargin wata ƙungiyar farar hula ta JTF ta sace iyayensu tare da miƙa su ga sojoji a ranar 30 ga watan Yulin 2013 amma sun rabu da iyayensu.
Cikin wazanda suka ɓace har da tsohon shugaban ƙaramar hukumar Gwoza, Hon. Bukar Musa Barawa.
Ya kuma bayyana cewa, “’yan gudun hijirar daga Gwoza ba su da damar samun ‘yancin siyasa, aikin yi, isassun kiwon lafiya, kuma ba a ba su haƙƙinsu ba.”
