An nemi a ciyar da malaman firamaren Kano gaba akai-akai

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Ƙungiyar Malamai ta Ƙasa reshen Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar akan ta yi ƙarin matsayin aiki, musamman ga malaman makarantun firamare, domin rabon da a yi musu an daɗe.

Shugaban ƙungiyar, Kwamred Abubakar Hambali, shine ya yi kiran a wajen bikin Ranar Malamai ta Duniya da aka gudanar a rufaffen ɗakin wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata a Kano ranar Talata.

Ya yi nuni da cewa, rabon da a yi wa malaman ƙarin girma tun a shekara ta 2017 lokacin da aka ciyar da malamai 50,000 gaba, inda hakan ya sa sun jajirce sun ga kuma nasara a wajen ɗalibai da suka zama jarrabawa a matakai daban-daban, saboda sun sami ingantacciyar tarbiyya da horo da koyo.

Kwamred Hambali ya ce, taron Ranar Malamai, Majalisar Ɗinkin Duniya ce ta keɓe dukkan ranar biyar a watan 10, domin farin ciki kan nasarori da malamai ke samu, sannan su gabatar da ƙudurori da matsalolinsu na koyo da koyarwa da yanda za’a magance a kuma tuna ’yan mazan jiya da kuma yi wa waɗanda suka riga gidan gaskiya a cikinsu addu’a da fatan alkhairi ga wanda suke a raye.

A jawabinta a madadin Gwamnan Jihar Kano, Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, Hajiya Lauratu Ado Ɗiso, ta ce, gwamnanatin Kano tana yaba wa malamai akan rawar da suka taka a lokacin ta’azzarar annobar cutar sarƙewar numfashi ta Korona wajen cigaba da bai wa yara ilimi.

Shi ma Babban Sakataren Zartarwa na Hukumar Makarantun Sakandire na Jihar Kano, Dr. Bello Shehu, wanda ya wakilci Kwamishinan Ilimi na jihar, ya ce, suna tabbatar wa malamai goyon baya da samar da yanayi na kyautata koyo da koyarwa kuma gwamnati a shirye ta ke ta yi amfani da shawarwari da aka bayar a taron.

A jawabinsa Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago na Jihar Kano, Kwamared Kabiru Ado Minjibir, ya gode wa malamai bisa dattakonsu da haƙuri da suke da kowane yanayi da suka sami kansu a ciki, sannan ya yi kira ga gwamnati da ta riƙa biyan albashin dukkan malamai daidai da na sauran ma’aikata, kamar yadda doka ta tanada ta sabon tsarin albashi.

A yayin taron dai Malam Bashir Mansur Malami na Tsangayar Ilimi daga Jami’ar Bayero ya gabatar da muƙala akan irin gudunmuwa da malamai ke bai wa raya zukata da ilimi.
An kuma bayar da shaidar yabo ta karramawa ga wasu da suka taka rawa sosai a fannin cigaban ilimi.