Shugaban malaman makaranta na Nijeriya ya bayyana dalilan rashin ingancin ilimi

Daga AMINU AMANAWA a Sokoto

Shugaban Ƙungiyar Malamai ta Ƙasa, Kwamred Nasir Idris, ya bayyana matsalar tsaro a makarantu, rashin aiwatar da mafi ƙankantar albashi ga ma’aikata da ma ƙarancin malamai a makarantu a matsayin wasu daga cikin ƙalubalan da ke cigaba da zama tarnaƙi ga malamai da ma ɓangaren ilimi ɗungurugum a Nijeriya.

Dr Nasir Idris ya dai bayyana hakan ne a cikin wani bayani da ya fitar, domin Bikin Ranar Malamai ta wannan shekarar, yayin da shugaban ƙungiyar malamai ta Jihar Sokoto, Kwamred Umar Moyi Tambuwal, ya gabatar a wajen taron da aka gudanar a makon nan a Sokoto, Babban Birnin Jihar, a madadinsa.

Dr Nasir ya bayyana cewa, ƙalubalen ba ƙaramar barazana suke ga cigaban ilimi ba, inda ya yi amfani da wannan damar wajen kira ga masu ruwa da tsaki kan su ƙara matsa ƙaimi, domin magance matsalolin da ke ci wa al’umma tuwo a ƙwarya. Ya kuma yi amfani da wannan damar wajen kira ga malamai kan su ƙara zage damtse wajen bayar da tasu gudunmawa, domin samar da yara nagari da ma ciyar da ƙasar gaba.

Shi ma da ya ke magana da Wakilin Manhaja bayan kammala taron, Shugaban ƙungiyar malamai na jihar, Kwamred Tambuwal, ya bayyana cewa, duk da irin ƙalubalen da ke ci wa malamai tuwo a ƙwarya a jihar, har yanzu su na iyaka nasu ƙoƙari wajen ciyar da al’umma gaba.

“Duk da irin ƙalubale da malamai ke fuskanta, musamman ma na ƙarancin albashi da warwala, har yanzu mu malamai mu na taka rawar a zo a gani, sai dai akwai buƙatar gwamnatoci su riƙa kulawa da gaskiyar halin da mu ke ciki tare da ɗaukar matakan tallafa ma na,” inji shi.

A zantawa da manema labarai a wajen taron, Kwamishinan Ilimi a Matakin Farko na Jihar, Alhaji Bello Abubakar Guiwa, wanda Shugaban Hukumar Kula da Malamai ta Jiha, Alhaji Bello Garba Yabo, ya wakilta, ya bayyana cewa, gwamnatin jiha na iyaka nata ƙoƙari, domin kyautata jin daɗi da warwalar malamai.

“Gwamnati na ɗaukar matakan da suka dace wajen inganta jin daɗi da warwala malamai, domin a nan Sokoto gwamnati na biyan malamai cikin lokaci da kuma kyautata jin daɗi da warwalarsu.”

Wakiliyar ƙungiyar Action Aid a Sokoto, Hajiya Halima Muhammad, kira ta yi ga Gwamnatin Jihar Sokoto da ta samar da tsarin albashi mai kyau ga malamai da ƙara ɗaukar malamai da ma horar da waɗanda ke kai a yanzu da samar da tsaftataccen ruwan sha ga makarantu da kuma samar da wurin zama da albashi na musamman ga malaman da aka tura yankunan karkara, domin koyarwa.

Taken Ranar Malaman na bana shi ne, ‘Malamai A Tubalin Farfaɗo Da Ilimi Daga Nakasu’.