Gudunmawar malamai ga harkar ilimi da cigaban ƙasa

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI

A duk shekara, Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware ranar 5 ga watan Oktoba, domin ta zama ranar da duniya za ta tuna da gudunmawar da malamai ke bayarwa wajen yaƙi da jahilci, koyar da ilimi ga yara masu tasowa da kuma horar da matasa da sauran masu nazari da bincike kan fannonin rayuwa daban-daban, domin su samu ƙarin ilimi da gogewa.

Tun daga shekarar 1994 da aka fara tsayar da wannan rana duniya ke bukin ta, wajen tattaunawa da nazarin yadda gwagwarmayar malamai da sadaukarwar su take samar da ilimi mai inganci, da ɗora al’umma a tafarkin cigaba ta hanyar wayar da kai da nuna musu abubuwan da suka kamata da waɗanda ba su dace ba, wanda rayuwa za ta inganta da su.

A wani sakamakon bincike da Hukumar UNESCO mai kula da harkokin ilimi, binciken kimiyya da fasaha da rayuwar ƙananan yara, da ke ƙarƙashin Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar an yi nuni da cewa, akwai yara kimanin miliyan 4 da dubu ɗari 5 da ke rayuwa a ƙasashen Afirka na kudu da Sahara, waɗanda ba su samu damar zuwa makaranta ba. Yayin da misalin kashi 52 cikin ɗari na yara mata a duniya ba sa samun damar shiga makaranta.

Ƙuduri na 4 na jerin ƙudurori 17 don samar da ingancin rayuwa a duniya, wanda shirin SDG na Majalisar Ɗinkin Duniya ya tsara da nufin cimma su nan da shekarar 2030, an sanya samar da ingantaccen ilimi a jerin muhimman abubuwan da za su samar wa ɗan Adam cigaba da inganta rayuwar sa. Daga cikin matakai 10 da aka yi la’akari da su a matsayin ginshiƙin cimma nasarar samar da ingantaccen ilimi akwai batun samar da ƙwararrun malamai da kyautata rayuwar su ta hanyar samar musu da muhallin koyarwa mai kyau, kayayyakin karatu, albashi mai kyau da tura su samun horo da ƙaro ilimi a kai a kai.

Amma anya kuwa malamai suna samun wannan kulawa da gatan da ya kamata, ba ma a Nijeriya kaɗai ba har ma da duniya baki ɗaya? Malamai na da matuƙar muhimmanci da tasiri a kowacce al’umma, amma ba kasafai ake kula da wannan martaba ta su ba. Sun kasance na bayan baya a jerin ma’aikata da ake ganin su da kima, a idon jama’a. Darajar aikin koyarwa kullum sai ƙara faɗuwa take yi, saboda yadda gwamnati da hukumomi ke yi wa harkar ilimi riƙon sakainar kashi.

A ƙasashen Afrika irin Nijeriya aikin koyarwa ya zama aiki mafi ƙasƙanci da duk wanda ya rasa aikin yi, sai ya shiga koyarwa a matsayin aikin mara aikin yi. Saboda rashin mutunci da martabar da ake yi wa masu aikin koyarwa. Masu makarantu waɗanda wasun su su ma da malamai ne, ba sa biyan malaman da ke koyarwa a ƙarƙashin su haƙƙoƙin su a kan lokaci, ko kuma biyan su wani abin kirki da zai rufa musu asiri, su da iyalan su. Wannan matsala ba ta tsaya ga makarantu masu zaman kansu kaɗai ba har ma da na gwamnati.

A cikin saƙon da ya aikewa ‘yan Nijeriya shugaba Muhammadu Buhari ta bakin Ƙaramin Ministan Ilimi Chukwuemeka Nwajiuba ya yi wa malamai albishir ɗin, nan da watan Janairu na shekara mai zuwa 2022 za a fara biyan malaman makarantun gwamnati da sabon tsarin albashi, wanda a cewar sa zai kawo ƙarshen cece kuce ɗin da ake ta faman yi na rashin ingancin albashin malamai. Wannan zai shafi batun alawus alawus ɗin malamai, tanadin mallakar gidaje, da samun ƙarin horarwa, har ma da ƙarin shekarun yin ritaya daga shekara 35 zuwa 40.

Malamai da dama a Nijeriya na ganin idan har wannan alƙawari na gwamnati ya tabbata to, malamai a ƙasar nan za su ji daɗi, kuma kima da martabar su za ta dawo a idon jama’a, ta yadda sai wane da wane ne zai iya samun damar shiga aikin koyarwa. Amma kuma wanne canji hakan zai yi ga harkar koyarwa? Da inganta albashin sauran malamai da ke ƙarƙashin makarantu masu zaman kansu? Idan aka lura yanzu, musamman a birane makarantun gwamnati sun zama kufayi, sai ‘yan ƙalilan ne suke da tasiri, inda za ka ga ɗalibai da malamai ana karantarwa. Domin kuwa akasarin iyaye sun fi sanya ‘ya’yansu a makarantun kuɗi ko na masu zaman kansu, don suna ganin nan ne yaran su za su samu koyarwa mai inganci.

Wani ƙarin ƙalubalen kuma shi ne na rashin samun gogewa a harkar koyarwa, domin kuwa ba duka malamai ne da ke makarantu masu zaman kansu suke da shaidar karatu ta NCE ba, wato shaidar da ke tabbatar da sun samu ƙwarewa ta musamman a harkar koyarwa.

Ko da yake jihohi da dama sun fara wannan yunƙuri na tantance malamai, da tabbatar da ingancin ƙwarewar su, amma akwai buƙatar ko bayan samun takardun shaidar karatu, a kuma ƙara mayar da hankali wajen ƙara horar da malamai muhimman dabarun koyarwa na zamani, domin su fahimci sabbin hanyoyin koyar da ilimi.

A cikin wannan shekara, harkar ilimi ta ci karo da wasu matsaloli masu yawa da suka riƙa gurguntar da cigaban da ake ƙoƙarin samar wa. Ɓullar annobar COVID-19 ta haifar da rufe makarantu, da mayar da koyarwa ta hanyar kafafen watsa labarai da kafofin sadarwar zamani, abin da ya sa tsarin koyarwa ya sake zama wani aiki mai wuyar sha’ani.

Ga batun matsalolin tsaro da suka tarwatsa iyalai da dama da mayar da wasu makarantun sansanonin ‘yan gudun Hijira. Ga ƙalubalen ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda da ke far wa makarantu suna sace ɗalibai suna garkuwa da su, don neman kuɗin fansa, abin da ke ƙara tsoratar da iyayen yara tura yaransu makarantun kwana ko waɗanda ke nesa da gida.

Ko a kwanaki ma sai da wata ƙungiyar ‘yan ta’adda da ake danganta ta da Boko Haram a Jihar Naija suka aika da wani saƙon gargaɗi a ƙauyukan da ke yankin Shiroro kan su daina kai yaransu makarantar boko, saboda ta saɓa da tsarin koyarwar addini.

Wannan irin barazana ba a kan ɗalibai kaɗai ta tsaya ba, har ma da malaman su, waɗanda sau da dama da su ake haɗawa a sace, a duk lokacin da ‘yan bindiga suka kai farmaki wata makaranta, da niyyar ɗiban ɗalibai.

A wannan shekara, bikin ranar ya mayar da hankali wajen duba yadda za a kyautata rayuwar malamai domin dawo da martabar ilimi. Taken da za a iya cewa ya zo a daidai lokacin da rayuwar malamai ke fuskantar ƙalubale mai yawa, tare da buƙatar haɗin kan hukumomi, ƙungiyoyin sa kai, da iyayen yara, da nufin ƙarfafa musu gwiwa.

Muna fatan gwamnatin tarayya za ta cika alƙawarin da ta yi wa malamai na fara ganin sauyi a albashin su, nan da sabuwar shekara mai zuwa, kuma mu ga gwamnatocin jihohi su ma sun yi koyi da haka, ba tare da ɗaukar dogon lokaci ba. Har wa yau da fatan su ma malamai za su yi amfani da wannan damar wajen qara kyautata ayyukansu, da inganta ilimin su na koyarwa, bisa sabbin tsare-tsaren koyarwa na duniya.