Tarbiyyar gida: Hisabi kan maza

Daga SADIYA GARBA YAKASAI

Dafatan ku na jin daɗin wannan filin namu mai albarka. Yau manyanmu zan taɓo, wato maza. Dalili kuwa, Ina jiyo kukan mata a kanku, ba a gida kawai ba, har a asibitoci, gidajen biki, tarukan suna, kotuna da ofisoshin Hisba.

Wallahi abin ya fara yawa. Yadda mata ke kokawa a kan rashin adalcin da maza suke musu kamar ba su taɓa sanin wata halitta mai motsi irin mata ba. Wallahi mata na cikin gararin rayuwa wanda duk mai imani ya gani zai koka. Amma su mazan, na ga ko a jikinsu. Wallahi ba ruwansu, ba su damu da irin baƙar rayuwar da matan su ke fuskanta ba. Ƙiri-ƙiri gidanka zai kama da wuta, kana gani ya ci, ya cinye, ba tare da ka duba wacce irin ɓarna wutar ta haifa maka ba.

Ko da, da laifin mata, to yanzu laifin maza nema yake ya danne na matan. Ba kuma komai ya jawo ba, irin rashin kulawa da ɗaukar matsalar iyali da muhimmanci. wanda dole dai duk tsiya abinda mace ta je ta ɗebo dole a raba da kai.

Wani kuma fa mazan ne silar ruftawar mace kowacce irin rayuwa. Don ba komai ke kawowa ba illa rashin sauke haƙƙin iyali da mazan yanzu ba sa yi sun fi karkata da cusguna wa mace da yaranta fiye da tausayawa da imani. Ina alkawarin da ka ɗauka na kula da ita da bu}atunta?

Duk da rayuwa ta yi tsada, amma bai kamata a ce ɗa namiji ya sakar wa mace mai rauni sha’anin gida ba. Duniyar Allah ta yaya za a ce mace ce a komai na rayuwar gidanka?
Sayen magani
Sayen audugar mata
Sayen wando
Sayen siket
Sayen rigar mama
Kudin makaranta da harkar rubutun kayan makaranta.
Dinkin kaya
Abinci, da sauransu. 

Duk waɗannan nauyi ne da Allah ya ɗora wa namiji ya sauke. amma sai ya yi buris, ya ce babu, kuma ba zai yi ba. Ita kuma uwa dole ta nema ta yi, muddin tana son yaranta su wadata kada su faɗa matsalar rayuwa ta bariki ,ko shaye-shaye.

To, amma yanzu iyaye maza su shagala sun ajiye koyarwar da iyaye suka ɗora mu a kai, kowa tasa ta fisshe shi. An sakar wa uwa ragamar gida ta ciyar da iyali kusan goma, a ɗari biyar. Wani ma ba awo, ba cefane. Ita ce kwal, shi dai zai ba da ɗari biyar ya shura takalma ya fita. Idan ba a yi sa’a ba ma,  shi ma idan ya dawo nasa abincin zai nema.

Da wannan rayuwar maza yanzu ke kuntatawa mata Wanda mata ƙalilan ke da wannan }wanjin iya tallafa wa mata bayin Allah.  Maza gumbar dutse kawai. Ka saki mace, ka tara mata da nauyin yaranka. Ba ci, ba sha, haƙurin zama kawai. Kai haƙƙoƙinka kake da tunanin wacce za ka kuma kwasowa.

Maza sai an yi haƙuri an yi dubaiyya,  an kau da kai. Ita da ma tarbiyya da ciyarwa, duk ibada ne. Sai an yi da gaske sannan za a ga hasken abun. Iyaye maza ɗai-ɗaiku ne suka san nauyin iyali mata. A duba zamani kowacce mace na buƙatar audugar mata wanda duk uba yana da kyau ya san wannan.

Duk da ta yi tsada, amma da yake sau ɗaya ne a wata, sai uba ya duba. Idan Uba kuma bai da halin, to uwa sai ta samu zani mai kyau ta kashe shi ta yanyanka wa yarinya ta koya mata yadda ake amfani da shi, da yadda za ta ba da awa ɗaya, biyu, sai ta cire, ta wanke, ta sa wani. Don shi abinda yake buƙatar tsafta ba a sa  tun safe ba a bar shi har washegari. Tsami zai yi ya yi ta wari. Ke ya dame ki, ya damu wani ma.

Duk irin wannan abun,  uwa ya kamata ta koya wa ɗiyar ta, yau da gobe, sai Allah fa. Ba Kullum uba zai iya saya ba, yadda komai yanzu ya yi tsada.

‘Yar sana’ar nan, mata yana da kyau su koya don kashe wa kai wasu lalurorin da ba sai sun jira miji ba. Ya danganta da yanayin da ake ciki yanzu. Dole iyaye su yi wa juna adalci, a kuma taimaka wa juna ta kowacce hanya don rufin asirin juna. Su ma kuma yaran a yi ƙoƙarin koya musu sana’ar don su tashi da ita su dogara da kansu, ba sai an musu ba.

Duniyar tamu ce ta zo a bai-bai. Sai masu imanin gaske.  Yanzu an kasa iya riƙon gida. Abin takaici a ce ka saki mace da yara kuma ka fitar da ita cikin gidanka, ka kuma haɗa ta da yaran, ba ci ba sha, ba suttura, ba kuɗin omo da sabulu. 

Kawai kai burinka ka cusguna mata. Wanda Ba ka san irin uƙubar da ka sanya ta ba. Haka za ta yi ta ɗawainiya ba tare da tallafawa ba. Ƙila ma ka manta da rayuwarta, da ta yaranka. Ba za ka taɓa tunawa da ita ba, sai dai idan tsautsayin hakan ya zo.

Su kuma matan ,su san ciwon kansu wallahi. Haka nan kawai namiji ya sake ki, ya kuma bar miki yaran. To ki kai su ina ? Ai kawai ki san madafa kafin ki tafi, ki tabbatar da tsaron yaranki da mahallinsu. Gurin wa ya cancanta ki bar su. Ba wai kawai ki ɗiba ki kai gidanku ba. Ciyarwa da buƙatunsu duk ya ba ki, sannan ki tafi. Amma ian ba wannan abubuwan, to ki share ɗakinki, ki yi zaman yaran ki.

Ba komai yanzu ake wa saki ba. Maza haƙuri da dubaiyya za ku yi. kar ki zauna ki bi dokin zuciya ki tafi da su, kuma su zame miki abun tausayi.

Cikin wannan rayuwar mata abun tausayi ne mazaje a tsaya a duba don Allah. Babu wata riba da za ka ci idan ka bar iyalanka cikin kulawar mace kawai. Tana ta haƙilon ba wa yaranka tarbiyya. Lokaci ɗaya kuma, tana kokarin kulawa da buƙatunsu. Kai a kan kanka idan ka nutsu, ka yi tunani, ka san ka takura wa iyalinka. Kuma, wallahi babu wani abu da za ka samu na jin daɗin rayuwa. Har gwara ma ka tsaya tsayin daka, ka kula da iyalin naka daidai iyawa.

Matsala ta gaba da za mu fuskanta, mu kuma sa ido yadda yaranmu mata ke mai da kansu sakarkaru agun samari. A kan abun duniya ka]an, yarinya sai ta ɓata rayuwarta, kuma hakan duk ya samo asali ne daga rashin wadatar da ba su samu ba, gurin iyaye. Sai su samu damar ɓata rayuwarsu gurinn miƙa wa samari lalurarsu. Wasu nagari su yi musu faɗa, wasu kuma sun samu abinda suke so Wanda duk wannan sakaci ne na iyaye wallahi. Idanun yara ya buɗe yanzu.

Komai kwance yake cikin ƙwakwalwarsu. a zuwan su dai-dai suke. Wanda hakan ba ƙaramin abu ba ne. An ɓata goma, ɗaya ba ta gyaru ba.
Allah ya sa iyaye mata da maza na biye da mu za su zama masu sa ido a kan gidansu, da yaransu, gudun barin baya da ƙura. Su kuma iyaye mata ba su sa ido, ba sai abun da yaransu suke so, za a yi ba.

Abun da muka yi na dai-dai Allah ya gyara mana. Wanda muka yi ba daidai ba, Allah ya yi mana afuwa.

Mu tara sati na gaba, idan Sarki mai dukka Ya bar mu. Ma’assalam.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *