Gwamna Sule ya rantsar da sabbin ciyamomi

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

An rantsar da sabbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin jihar Nasarawa su 13 bayan kammala zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a Larabar da ta gabata.

Gwamnan jihar, Injiya Abdullahi A. Sule ne ya rantsar da ciyamomin a fadar gwamnatin jihar da ke Lafia, babban birnin jihar a jiya Juma’a.

Yayin rantsarwar, Gwamna Sule ya nusar da sabbin ciyamomin da su sani wannan wata muhimmiyar dama ce suka samu don bada gudunmawarsu ga cigaban jihar da ma al’ummarta.

Don haka ya hore su da su yi aiki bilhaƙƙi tare da kwatanta adalci wajen sauke nauyin al’umma da ya rataya a kansu ba tare da nuna bambaci ko wariya ba.

Da yake bayyana sakamakon zaɓen, Shugaban Hukumar Zaɓen Jihar, Barista Ayuba Wandai Usman, ya ce an gudanar da zaɓen ne a tsakanin ƙananan hukumo 13 da kuma gundumomi (wards) 147 da jihar ke da su.

Ayuba Wandai Usman

Tare da cewa, bisa rahotannin da suka samu, zaɓen ya gudana cikin nasara ba tare da fuskantar wata matsala ba, in ban da ƙalubalen jinkirin da aka samu wajen isan kayan zaɓe zuwa rumfunan zaɓe.

Ya ci gaba da cewa, jami’yyu guda bakwai ne suka fafata a zaɓen da suka haɗa da: ADC, APC, NNPP, PDP, SDP da kuma jam’iyyar ZLP.

A ranar Larabar da ta gabata al’ummar jihar Nasarawa suka fito don zaɓen ciyamomi da kansilolin da za su ci gaba da jan ragamar harkokinsu nan da shekaru uku masu zuwa.

Jihar Nasarawa jiha ce da ta ƙunshi ƙananan hukumomi guda 13, su ne: Akwanga, Awe, Doma, Karu, Keana, Keffi, Kokona, Lafia, Nasarawa, Nasarawa Eggon, Obi, Toto da kuma Wamba.

Gwamna Sule
By Editor