An rufe Jami’ar Tarayya ta Lokoja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Gudanarwar Jami’ar Lokoja ta Jihar Kogi ta sanar da rufe makarantar, biyo bayan mutuwar ɗalibai guda biyar a yayin wani hatsari.

A ranar Litinin ne Rajistirar Jami’ar, Dakta Rebecca Aimiohu Okojie ta bayyana hakan a wata takarda da fitar, inda ta zayyano kwamishinan ƴan sandan jihar da daraktan Hukumar DSS aciki.

Haka kuma a ranar ta Litinin, 17 ga watan Fabrairu ne wani hatsarin tirela ya yi sanadin mutuwar ɗaliban jami’ar biyar a Birnin Felele.

Lamarin da ya harzuƙa sauran ɗaliban, inda suka yi gangami a ƙofofin jami’ar duk cewa gwamnatin jihar da Hukumar gudanarwar sun shiga tsakani don kwantar da hankulansu.

Ganin yadda lamarin ke ƙara ƙamari, an samu shawarwari daga hukumomin tsaro sakamakon fargabar ƙara samun wasu mace-macen, wanda hakan ya sa aka ga dacewar rufe makarantar.

Sanarwar ta kuma umarci ɗaliban da su fice daga makarantar kafin ƙarfe 12 na ranar Alhamis.

By Babaji