An samu gawar lakcara ‘yar Nijeriya a gidanta na Afirka ta Kudu yayin sababbin hare-haren ƙyamar baƙi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An samu gawar wata malamar jami’a mai suna Ayodele Odularu, wadda ke karantarwa a Jami’ar Fort Hare da ke Afirka ta Kudu a gidanta na Estern Cape Province a ƙasar.

Rahotanni sun bayyana cewa, Odularu ta rasu ne a ranar 16 ga Agusta bayan shafe shekaru 51 a duniya, kamar yadda ɗan uwanta Gbadebo Odularu ya shaida wa manema labarai a ranar Asabar.

Ya ce, suna tunanin mutuwarta tana da alaƙa da wani ɓoyayyen al’amarin, musamman ganin yadda ba su gano ainihin yadda ajalin nata ya riske ta ba. Akan haka ne iyalanta suke kira ga mahukunta da a gudanar da bincike akan rasuwarta tare da fitar da sakamako a kai.

A cewar wata sanarwa da Gbedebo ya wallafa a madadin iyalan, ana bayyana lakcarar a matsayin, wadda ta sadaukar da rayuwarta ga ilimi, bincike da ƙoƙarin samar da yanayi mai kyau ga al’umma, yana mai cewa rayuwarta za ta cigaba da yin tasiri akan mutanen da ta inganta rayukansu.

A ranar Alhamis ne jami’ar University of Fort Hare ta shirya wani taro domin karrama malamar sakamakon hidimarta ga fannin ilimi musamman a jami’ar.

Mutuwar wannan malama dai ta auku ne a daidai lokacin da ake tsaka da kai kai farmaki kan ‘yan Nijeriya da ‘yan wasu ƙasashen Afirka a Afirka ta Kudu sakamakon ƙyamar baƙi daga wasu ‘yan ƙasar.

Tun a watan Yunin 2026 ne Nijeriya ta ƙaddamar da shirin kwaso ‘yan da ke Afirka ta Kudu kan hare-haren ƙyamar baƙi, inda zuwa yanzu ta ɗebo jimillar mutane 1,716 daga ƙasar zuwa Nijeriya.

By Babaji

Leave a Reply