An yanke wa jagororin Ansaru biyu hukuncin ɗaurin rai-da-rai bayan gano suna da hannu a sace ‘yan Oyo

Spread the love

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yanke wa wasu manyan jagororin ƙungiyar Ansaru biyu hukuncin daurin rai da rai bayan sun amsa laifukan ta’addanci 32 da hukumar DSS ta tuhume su da su.

Waɗanda aka yanke wa hukuncin sun haɗa da Mahmud Usman (Abu Bara’a), wanda ake zargi da jagorantar Ansaru, da mataimakinsa Abubakar Abba (Malam Mamuda).

Mai shari’a Emeka Nwite ya ce ya yi la’akari da roƙon da lauyansu ya gabatar kafin ya yanke hukuncin.

Kotun ta yanke musu daurin rai da rai kan laifukan ɗaukar nauyin ta’addanci ta hanyar amfani da kuɗaɗen haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da kuma kuɗin fansar garkuwa domin sayen makamai da abubuwan fashewa.

Haka kuma ta yanke musu hukuncin ɗaurin shekaru 20 kan sauran mafi yawan tuhume-tuhumen, tare da ƙarin shekaru 15 kan wasu laifuka, inda kotun ta umarci hukuncin ya fara aiki tun daga ranar da aka kama su.

An gurfanar da su ne tun watan Satumban 2025 bayan kama su a wasu samame tsakanin Mayu da Yulin 2025. Bayan sun fara musanta zarge-zargen, daga bisani sun sauya matsayinsu tare da amsa dukkan tuhume-tuhumen.

DSS ta ce mutanen sun shiga cikin ayyukan ɗaukar nauyin ta’addanci, satar mutane domin karɓar kuɗin fansa, haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, ƙera bama-bamai da kuma jagorantar hare-hare, tare da alaƙa da ƙungiyoyin ta’adda masu alaƙa da Al-Qaeda a yankin Sahel.

Kazalika, ana zarginsu da hannu a hare-hare da sace-sacen mutane da dama da suka faru a sassan Nijeriya.

By Babaji

Leave a Reply