Ana buƙatar jam’iyyar hamayya mai ƙarfi a dimokuraɗiyya – Gbajabiamila

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Shugaban ma’aikata na fadar gwamnatin Nijeriya, Femi Gbajabiamila ya ce haɗakar ‘yan siyasa a jam’iyyar ADC alheri ce ga siyasar Nijeriya, wanda a cewarsa hakan zai taimaka waje hana ƙasar faɗawa cikin siyasar jam’iyyar ƙwaya ɗaya tal.

Gbajabiamila ya bayyana haka ne jim kaɗan ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomin da aka yi a jihar Legas a ranar Asabar a mazaɓarsa da ke Surulere, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sai dai tsohon shugaban majalisar wakilan ƙasar ya bayyana shakkunsa kan haɗakar, inda ya ce ce ba ya tunanin za ta yi wani tasirin a-zo-a-gani.

“Muna maraba da samar da haɗakar. Ai ba wannan ba ne karo na farko da aka samu haɗakar ‘yan siyasar a wannan ƙasar tamu,” inji shi.

Ya ƙara da cewa “a dimokuraɗiyya ana buƙatar hamayya mai ƙarfi, domin idan babu hamayya mai ƙarfi, za mu iya faɗawa siyasar jam’iyyar ɗaya,” inji shi.

A Nijeriya dai fitatun ‘yan jam’iyyun hamayya irin su Atiku Abubakar da Peter Obi da Nasir El-Rufai da Rotimi Amaechi da sauransu ne suka haɗu a jam’iyyar ADC domin fuskantar zaɓen 2027, inda suke fata za su kayar da Bola Tinubu.

By ukarofi