Ana zargin Matawalle da hannu a tsare wadda ta yi ikirarin masoyiyar Tinubu ce – Majiyar tsaro

Spread the love

Wasu sabbin bayanai sun bayyana a game da kamawa da tsare Maryam Bukar, wadda ake zargin ta taɓa yin alaƙar soyayya da shugaban Bola Tinubu.

Majiyoyi sun shaida wa jaridar DAILY NIGERIAN cewa an tsare Maryam Bukar a wani sansanin soja na tsawon watanni takwas ba tare da damar ganin lauyoyi ko iyalanta ba, inda ake zargin hakan ya faru ne bisa umarnin karamin ministan tsaro, Bello Matawalle.

A ranar 19 ga Fabrairu, wani rahoto da kafar yada labarai ta Sahara Reporters ta wallafa ya zargi Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, da tsare matar bisa zargin yin kiran bidiyo na sirri da shugaban ƙasar.

Sai dai majiyoyin tsaro da suka san yadda lamarin ya gudana sun musanta cewa Ribadu na da hannu a kama matar. Wata majiya ta ce, “Zan iya tabbatar maka cewa Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro ba shi da masaniya kan kama ta. Wasu jami’an gwamnati na ambaton sunansa ne domin rufe gaskiya.”

Majiyoyin sun ce an ɗauki hoton bidiyon kiran ne tun kafin Tinubu ya zama shugaban ƙasa, amma an ce ministan bai ji daɗin yadda matar ta wallafa bidiyon ba.

A cewar majiyoyin, ana zargin Matawalle ya shirya kama Maryam Bukar ne ta hannun wata rundunar soja ta musamman. Sun kuma yi ikirarin cewa salon kamun da tsarewar ya yi kama da wasu lokuta da ake zargin ministan ya bayar da umarnin kamawa da tsare masu sukar sa da abokan adawarsa daga Jihar Zamfara.

“Ku tuna cewa Matawalle ya sha bayar da umarnin kamu da tsare masu sukar sa da abokan hamayyarsa daga Zamfara, yana amfani da matsayinsa na minista”, inji wata majiya.

Majiyoyin sun kuma kwatanta lamarin da kama Saleem Abubakar, wani mai ba gwamnan Zamfara shawara kan harkokin fasaha. Sun ce a wancan lokaci ma, da farko an zargi Ribaɗu, amma daga baya aka ce Matawalle ne ke da hannu.

Da aka tuntuɓi mai taimaka wa Matawalle kan harkokin yaɗa labarai, Ahmad Ibrahim Ɗan-Wudil, ya musanta zargin, yana mai cewa ubangidansa ba shi da hannu a lamarin kuma bai san komai a kai ba.

“Ba ma ma da masaniya kan wannan batu, kuma ba abin da muka sani akansa” inji Ɗan-Wudil”, kamar yadda jaridar ta ruwaito.

By Babaji