Atiku, Obi, ministocin Buhari da tsofaffin shugabannin APC sun karɓi jam’iyyar ADC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Yayin da ake cigaba da shirin tunkarar babban zaɓen 2027, haɗakar ƴan siyasar adawa ta karɓi jagorancin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a hukumance, ranar Laraba.

A taron, an ga wasu daga cikin ministocin da suka yi aiki da gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari da mambobin kwamitin ayyuka na APC.

Haka kuma, an gudanar da taron ne a ɗakin taro na Yar’Adua Centre dake birnin Tarayya Abuja, inda Shugaban jam’iyyar, Cif Ralph Nwosu ya ce ADC ta gudanar da zaman kwamitin zartarwa (NEC) guda 12 a cikin watanni 18.

Ya ce, Nijeriya ta shiga halin tsaka-mai-wuya don haka tana buƙatar ɗauki wajen dawo da martabarta.

Shugaban, tare da Sakataren jam’iyyar, Alhaji Saeed Baba Abdullahi ne suka jagoranci NEC na jam’iyyar a taron.

Daga nan ne aka naɗa tsohon shugaban Majalisar Dattawa, David Mark a matsayin shugaba na riƙon ƙwarya da tsohon gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola a matsayin sakataren jam’iyyar shi ma na riƙon ƙwarya.

A lokacin da ya ke jawabi, David Mark ya zargi Shugaba Bola Tinubu da zama sababin sanya ƴan Nijeriya cikin matsi duba irin tsarinsa waje tafiyar da mulkin ƙasar.

Ya ce, Tinubu yana yin duk mai yiwuwa wajen ganin ya mayar da Nijeriya ƙasar da ake mulki da jam’iyya ɗaya kaɗai ta yadda al’umma za su kasance ba su da zaɓi a 2027.

Jiga-jigan ƴan siyasar da suka halarci taron sun haɗa da Atiku Abubakar, Peter Obi, Datti Baba Ahmed, Aminu Waziri Tambuwal, Liyel Imoke da kuma Injiniya Babachir Lawal.

Daga mambobin kwamitin ayyuka na APC akwai Cif John Odigie-Oyegun, Malam Bolaji Abdullahi, Sanata John James da kuma Salihu Mohammed Lukman.

By Babaji