Ba za a bar Kano baya ba wajen yin rijistar zaɓe – Sheikh Tijjani Auwalu

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Yawan malamai da masana da yawan al’umma da Ubangiji ya albarkaci Kano da shi da kuma wayewar siyasa da sauran al’amura da kowa ya san Kano tana da wannan baiwar na cewa mutanen Kano wayayyayu ne ba za su yarda a barsu a baya ba na yawan katin zaɓe da hukumar zaɓe ta fara yi a yanzu haka, da ake ganin kamar za a bar Kano a baya, Kanawa ba za su yarda da wannan haƙƙi ba, kuma nasan halinsu za su tashi tsaye su je su yi rijista fiye da yadda ake tunani musamman yadda gwamantin Kano bisa jagorani gwamnan jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ɗauki mataki na kafa kwamitin wayar da kan jama’a domin a fita a yi rijista zaɓe, wannan na daga cikin dalilan da shi ma zai sa Kano ta riƙe kambunta na ko da mai ka zo an fi ka batun wasu jihohi sun fi Kano a yanzu tamkar tashin gishirin andar suka yi ita kuma Kano kamar sukuwar dawaki ne wani tashi a guje daga a ƙarshe na gaba ya koma baya haka Kano za ta yi wa jihohin Nijeriya fintinkau da ikon Ubangiji kamar yadda Kwamishinan Al’amuran Addini na Jihar Kano Hon Tijjani Sani Auwalu ya bayyana a lokacin da yake ganawa da manema labarai a birnin Kano.

Har ila yau ya ƙara da cewa duk da wannan hashashe da ya yi bisa sanin da kishi da wayewar mutanen Kano da ya sani amma wannan ba ta hana ya kira da malam, limamanmu, ‘yan kasuwarmu, da sauran al’umma cewa su fito su yi katin zaɓe ba saboda muhimmancinsa a siyasance da sauran mu’amala ta yau da kullum musamman Kano da ta zama cibiyar kasuwanci cibiyar siyasa wacce Malam Aminu Kano ya koyarwa al’umma Kano naƙi na duk wanda ya zo da wani na rashin gaskiyadon haka muna jaddada kira ga limamai da sauran masu ruwa tsaki ya cigaba da faɓakarwa da jamaa a masallatai da gurin tarurruka amfani wannan yin rijistar katin zaɓe.

Haka kuma ya yi amfani da wannan dama wajen nuna farin cikinsa da ganin wannan wata mai albarka wanda a cikinsa aka haifi fiyayyen halitta wanda kuma ya yi amfani da wannan wajen faɗakar da al’umma Musulmai muhimmacin maulidi da kuma yadda ya kamata a yi shi cikin tsari da dokokin shari’ar Musulinci da zamantakewa domin da cewa da yardar ubangiji cikin wannan wata mai albarka inda kuma ya yabawa alumma musulmi kan saudakrwa da suke yin a shirya tarurrukakan maulidi wanda ake yin hidima ta raba kyatuttuka da dafe-dafe da yanke yanke a tsayin sadaka domin neman yardar ubangiji inda ya yi nasiha da cewa akwai buƙatar a yi amfani da wannan dama wajen addu’o’in neman zaman lafiya, ƙaruwar arziƙi a Kano da Nijeriya baki ɗaya.

By ukarofi