Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Kebbe/Tambuwal a jihar Sakkwato, Abdussamad Dasuki, ya bayyana cewa ba zai sake neman takara a zaɓen 2027 ba, yana mai cewa lokaci ya yi da matasa za su karɓi ragamar shugabanci.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Dasuki ya ce matakin da ya ɗauka wata sadaukarwa ce domin ƙarfafa dimokuraɗiyya da kuma buɗe dama ga matasa su shiga siyasa.
Ya bayyana cewa shawarar ba ta samo asali daga gajiyawa ba, sai dai daga imani da hangen nesa na samar da sabon ƙarni na shugabanni.
Dasuki, wanda ya fara harkar siyasa tun 2011, ya taba zama ɗan majalisar dokokin Sakkwato, kwamishina a majalisar zartarwa, kuma yanzu yana wakiltar Kebbe/Tambuwal a majalisar tarayya.
Ya kafa The Future Is Now Project, wata ƙungiya da ke fafutukar ganin cewa kashi 70 cikin 100 na kujerun majalisar wakilai su kasance a hannun matasan ƙasa da shekaru 40 nan da 2027.
Ya gode wa al’ummarsa da jagoransa, tsohon gwamnan Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, bisa goyon bayansu, tare da kira ga matasa da su tsaya tsayin daka su yi jagoranci da gaskiya da hangen nesa.
